Search
Subscribe
Sayar da takardar daukar aiki ta fi sayar da makami illa

Sayar da takardar daukar aiki ta fi sayar da makami illa

 

Ashe har an kai lokacin da za a hana dan talaka aiki a Najeriya? Eh, haka ne mana saboda yadda masu hali da isa suka nuna haka abin yake. Saboda ana tufka tana warwarewa ne lura da yanayin rayuwar matasa masu neman aiki. Abin akwai ban-tausayi musanman dan talaka wanda ba ya da abin da zai ci balle ya cire makudan kudi ya sayi takardar daukar aiki.

Hakika rayuwar dan Najeriya tana cikin hadari kwarai da gaske matukar Gwamnatin Tarayya ba ta sanya dokar ta-baci ba, to za a samu masifar da ta fi ta Boko Haram.

A ganina sayar da takardun daukar aiki da wadansu masu isa suke yi, ta fi lalata kasa fiye da Boko Haram, domin wancan an san masu yi har ana iya yakarsu amma wannan illar da wadansu suka bullo da ita za ta iya zama makasudin lalata rayuwar dan talaka mai kada kuri’a in zabe ya zo. Sannan tana kashe gwiwar matasa  masu hazaka wajen neman aiki. Dan talakan da da kyar ya gama jami’a sannan wai aiki ma sai ya saya? Ka hana mu wuta da ruwa da hanyoyi da kiwon lafiya, shiru babu wani ayyukan ci gaba kuma a ce  takardar daukar aiki ma sai na saya? To ashe idan mutum ya aikata aikin ta’addanci ’yan siyasa ne suka ingiza shi domin ba wata doka a kasar nan da ta bada dama a sayar da takardar daukar aiki balle har wani ya ji wai ya burge ka don ya ba ka takardar.

Dalilina a nan shi ne duk wanda ya gama jami’a ko wata makaranta da za ta kai shi matakin neman aiki a kasa, to burinsa shi ne ya ga ya nema ya samu. Amma babban kalubale a yau a kasar nan shi ne sayar da takardun daukar aiki ta zama wani bangare na cinikayyar ma’aikata a boye wanda illar wannan abu ya fi illar daukar makami. Yau a Nijeriya  ne ake sayar da takardar daukar aiki daga Naira dubu 100 zuwa miliyan daya kuma duk da haka ba ka da tabbas na wanda zai sayar maka saboda ’yan uwansu gurbatattu sun shiga sahun sayar da na jabu. Ina kira ga Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi su dakile alakar tsakanin ’yan siyasa da bada takardar daukar aiki domin ta nan ne suke ganin sun yi kokari wai da sunan sun samar wa mutane aikin yi wanda a al’ada ta kasar nan in ka gama karatu neman aiki za ka yi a inda kake bukata ko inda aka tallata a jaridu idan da rabo sai ka samu.

Dawowar dimokuradiyya a Najeriya aikin gwamnati ya zama na sayarwa duk da cewa Shugaban Kasa Buhari a yanzu yana matukar kokari wajen ganin an daina haka amma miyagun fili da na boye suna amfani da damarsu suna aikata abin da suka ga dama. Mafita ita ce gwamnati ta ba ma’aikatu karfi wajen daukar aiki ta kuma kafa kwamiti na amintattun mutane daga cikin al’umma wadanda za su kasance suna kula da duk yadda aikin zai gudana.

Amma muddin aka ci gaba da barin ’yan siyasa suna sayen takardun daukar aiki to ina tabbatar da cewa dan talaka sai dai in rabo ya rantse kawai amma cancanta ba za ta taba kai shi ga samun aiki ba. Ina kira ga Shugaban Kasa da gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi su tashi tsaye su yaki wannan  matsala don ceto al’umma daga mugun halin da suke ciki. Fatata ita ce Allah Ya sa a gyara wannan babban kalubalen da ake ganinsa ba komai ba, amin.

Abubakar Muhammad Zain Imel:badfresh@gmail.com  (08035812895)

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin