✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sepp Blatter ya ba Cristiano Ronaldo hakuri

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) Mista Sepp Blatter a ranar Talatar da ta wuce ne ya ba shahararren dan kwallon Real Madrid da…

Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya (FIFA) Mista Sepp Blatter a ranar Talatar da ta wuce ne ya ba shahararren dan kwallon Real Madrid da ke Sifen Cristiano Ronaldo kan katobarar da ya yi na cewa dan kwallon ya fi mayar da hankali ne a kan gyaran gashi fiye da Messi, da hakan ta sa  Lionel Messi ya fi shi cancantar lashe gwarzon dan kwallon duniya.
Blatter a jawabin da ya yi a lokacin yin muhamara a tsakanin ’yan kwallon biyu na wanda ya fi cancantar lashe kyautar a Jami’ar Odford da ke Ingila a karshen makon jiya, ya bayyana cewa dalilin da ya sa Lionel Messi ya fi Ronaldo cancantar lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya shi ne Ronaldo ya fi mayar da hankali wajen gyaran gashi fiye da Messi, don haka a nasa ra’ayin ya gwammace ya zabi Messi fiye da Ronaldo.
Wannan kalami bai yi wa Ronaldo da kulob din Mardrid dadi ba, inda tuni suka aika masa wasikar neman gafara ga dan kwallon.
Sepp Blatter ya ce ya yarda ya yi kuskure, inda ya yi alkwarin hakan ba za ta sake faruwa.  Ya ce ya yi wannan kalami ne a bisa raha, ba wia da gaske yake ba amma idan sun bata ran Ronaldo da kulob din Madrid to yana neman su yafe masa.