Da Dumi Dumi

Shari’ar Atiku da Buhari: Shaidu sun fara bayani

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar

Shaidu sun fara bayani a gaban Kotun Sauraren Karar Zaben Shugaban Kasa a Abuja a karar da dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kai yana kalubalantar nasarar Shugaban Buhari a zaben da ya gabaata.                                                                                                                                                Wata shaidar da Jam’iyyar PDP ta gabatar Misis Ijeoma Peter Obi wadda ta nace cewa sun tura sakamakon zaben zuwa rumbun, sai dai ta gaza bayyana lambar sirrin da ta yi amfani da ita wajen tura sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun bana.

Obi wacce ta ce ita kwararriya ce a fannin sadarwar zamani ta ce ta tura sakamakon zaben ta nau’rar zamani zuwa rumbun INEC daga mazabarta a matsayinta na jami’ar kula da gyaran na’urar da ta sami horo daga Hukumar INEC. Shi kuma Adejuwitan Ebenezar Olalekan cewa ya yi ya tura sakamakon zaben ne ga rumbun adana bayanai na Hukumar INEC, inda ya shaida wa kotun cewa aika sakamakon zaben ga rumbun adana bayanai na hukumar kai- tsaye yake, kuma yana tafiya ne kai-tsaye daga na’urar dangwala yatsa domin tura sakamakon.

Sai dai da Lauyan Shugaba Buhari, Wale Olanipekun ya tambayi shaidar, cewa ya yi shi bai san Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shi ne mutum na biyu cikin wadanda Atiku yake kara ba, hakazalika a wata tambaya da Lauya Fagbemi ya yi wa shaidar ya tabbatar da cewa shi bai yi aikin zabe ba, sai dai kawai yana daya daga cikin wadanda  hukumar zaben ta kafe sunayensu domin yin aikin.

Idan dai za a iya tunawa an kira shaidun Jam’iyyar PDP ne, domin su ba da shaida a kan zargin magudin zabe da cin hanci da kura-kurai da karya ka’idojin zaben da Shugaba Buhari ya samu nasara a karo na biyu.

Shaida na farko da aka gabatar Alhaji Buba Galadima cewa ya yi yana goyon bayan Buhari tun a zaben shekarar 2003 zuwa 2015, amma ya kaurace masa ne saboda ya kasa cika alkawuran yakin neman zabe da ya yi ga al’umma. Buba Galadima ya ce ya koma goyon bayan Atiku ne, a 2019 saboda shi ne dan takarar da ya fi cancanta, kuma mai ilimi da tsoron Allah wanda zai iya gudanar da shugabancin da jama’a ke bukata. Sai dai ya ki amincewa da cewa ya kaurace wa Buhari ne, domin an hana masa wata dama, inda ya ce ya rabu da Buhari ne domin ya gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar wannan kasa.

ADVERTISEMENT

Da Lauyan APC Lateef Fagbemi, ke tambayarsa, Buba Galadima ya shaida wa kotun cewa shi ba dan Jam’iyyar PDP ba ne, sai dai jam’iyyarsa ta RAPC tana da kyakkyawar alaka da Atiku da kuma PDP a kan yadda za a samar da sahihin shugabanci da zai kula da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Haka wani shaidar da Jam’iyyar PDP ta sake gabatarwa a zaman kotun da ya gudana a ranar Talatar da ta gabata, Yusuf Salisu Majigiri wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Katsina ya shaida wa kotun cewa sun tura wakilan jam’iyyar 4,902 a rumfunan zabe a fadin jihar, inda suka zo musu da sakamakon zaben da ke nuni da cewa Jam’iyyar PDP ta samu kuri’a dubu 905, ita kuma APC ta samu kuri’a dubu 872. Yusuf ya ce sakamakon da hukumar zabe ta bayar ya sha bamban da ainihin wanda suke da shi,wanda hakan ya ba da nasara ga wanda suke bukata. Ya ce wannan ita ce matsalarsu, amma ba wannan na’ura ba ko alkaluman da hukumar zabe ta bayyana, domin sakamakon da ta bayyana ba shi ne wanda jama’a suka kada ba a zaben.

Lauyoyin da ke kare wadanda ake kara, Yunus Ustaz Usman (SAN) da Wole Olanipekun (SAN) da Lateef Fagbemi (SAN) sun tambayi shaidar cewa shin ya ji jawabin da Shugaban Kasa ya yi cikin Ingilishi mussamman lokacin da yake Shugaban Kasa na Soja a1983, sai ya ce bai ji ba domin a lokacin yana kauyensu, amma dai ya ji na Janar Sani Abacha.