✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar sanya hijabi a makarantun Legas ta dauki sabon salo

Wasu dalibai mata biyu da hadin gwiwar kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya sun kai gwamnatin Jihar Legas kara a babbar kotu da ke yankin Ikeja…

Wasu dalibai mata biyu da hadin gwiwar kungiyar dalibai musulmi ta Najeriya sun kai gwamnatin Jihar Legas kara a babbar kotu da ke yankin Ikeja kan zargin cin zarafin da shugaban makarantarsu ta yi musu saboda sun sanya hijabi.
To amma rashin zuwan alkalin kotun, Mai shari’a Olubunmi Oyewole ya sanya an dage ci gaba da sauraren karar zuwa ranar 28 ga watan Oktoba mai zuwa.
daliban da suka shigar da karar da ake kira Miss Asiyat Abdulkareem da Miss Maryam Oyeniyi sun nemi kotun ta nema musu hakkinsu kan cin zarafin da shugabar sakandarensu da ke unguwar Surulere, mai suna Misis Oyefeso, ta yi musu saboda kawai sun sanya hijabi a harabar makarantar.
Idan ba a manta ba a ranar 27 ga watan Mayun da ya gabata, al’ummar musulmi mazauna Jihar Legas sun shigar da kara babbar kotun da ke yankin Ikeja suna kalubalantar gwamnatin jihar na hana dalibai musulmi sanya hijabi a harabar makarantun jihar.
A lokacin da aka ambaci karar a gaban alkalin kotun, Mai shari’a J.O.K Oyewole, lauyan gwamnatin jihar,  Samuel A. Ajanaku ya bayyana cewa tuni gwamnatin jihar ta nemi a sasanta a wajen kotu.
To amma jagoran lauyoyin  al’ummar musulmin Jihar Legas, Barista Hassan A. Fajimite ya yi mamakin yadda gwamnatin jihar ta dage da a sasanta a wajen kotu.
Daga bisani alkalin kotun, Mai shari’a Oyewole ya bukaci bangarorin biyu su zauna su tattauna da juna kuma su sanar da kotun matsayar da suka cimma kafin karshen watan da muke ciki.
Jama’a da dama na yi wa shari’ar kallon zakaran-gwajin-dafi kan irin yadda tsarin ilimin boko na jihar ke yi wa wasu ka’idojin addinin Musulunci karan-tsaye a jihar.