Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Shawara ga Gwamna Masari

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari har yanzu dai ba zan gajiya da ba ka shawara ba. Ashekarar 2015 da ka ci zabe na ba ka shawara musamman a wannan jarida da sauran kafafen watsa labarai na gida da waje kamar Rediyon Jamus DW Hausa da Muryar Amurka BOA da sauransu, inda na ba ka shawarar cewa ya kamata ka zabo mutane nagari da za su taimaka maka wajen tafiyar da mulkin jiharmu. Sai dai kamar yadda dimbin jama’a ke maganganu a kan mataimakanka, jama’ar ba su gamsu da masu tallafa maka din ba. Wanda hakan ke nuna cewa ba ka yi aiki da shawarar da na ba ka. Duk da haka ba zan gajiya ba ko in yi kasa a gwiwa ba, zan ci gaba da ba ka shawarar.Ya kamata ka yi tsayin daka wajen ganin ka zabo mutane nagari masu mutunci da kima ga jama’a. Kada ka dauko wa kanka kara da kiyashi, ko ’yan ga mu mun iya. Ko ’yan da mu aka yi yakin neman zabe ko kuma ’yan hana ruwa-gudu.

Da fatan za ka zabo sahihan mutanen da za su tallafa maka wajen kawo wa jiharmu ci gaba. In ko har ka ci tuwon yau da miyar jiya tabbas sai cikinka ya gurbace. Kuma rawar ba za ta canja ba.

ADVERTISEMENT

 

Daga Shugaban Kungiyar Muryar  Jama’a, Haruna Muhammad Katsina.

ADVERTISEMENT

07039205659 08055887110

a2018@gmail.com