✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shaye-shaye tsakanin matan aure

Assalamu alaikum. A yau ma na sake dawo da wata takaitacciyar kira da nake son yi ga ma’aurata a kan wani mugun hali da yake…

Assalamu alaikum. A yau ma na sake dawo da wata takaitacciyar kira da nake son yi ga ma’aurata a kan wani mugun hali da yake neman zama ruwan dare a gidajen aure, ba tare da sanin masu gida ba.

Wannan matsalar ita ce matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da wadansu matan suke yi. Yanzu matan aure da dama sun shiga wannan mugun hali, ko dai ta hannun kawaye ko makwabta ko wadansu mugayen mutane da watakila aka hadu da su a gidajen suna ko biki ko makaranta.

Da yawa in ka tambaye su dalilinsu na shaye-shaye sai su ce maka wai idan sun shiga damuwa, kawai suna bukatar su ‘dauke wuta’ ne domin su dan samu su sarara. A cewarsu, hakan yana sanyawa su huce takaici kuma su daina shiga damuwa na wani dan lokaci. Za ka gansu yawanci suna zuwa shagunan magani da sunan sayan maganin zazzabi, amma kuma za ka ba su yarda a je asibiti a duba su, ballantana a ba su maganin ingantacce.

Wata mata ta fada min cewa kawarta ce ta koya mata cewa idan matsalar gida ko miji ta mata yawa, damuwa ta rufe ta, har ta rasa yadda za ta yi, to idan ta sha kwaya, za ta yi barci kuma za ta manta da duk abin da yake damunta.

Abin da wadannan matan ba su gane wa shi ne, wannan ‘dauke wutar’ da suke yi, na wani dan lokaci ne kawai. Kuma da sun farka daga barci, komai zan dawo danye.

A lokuta da yawa idan ka ga mata sun taru suna nuku-nuku, watakila babu abin da suke tattaunawa ko shiryawa sai maganar sayo kwaya ko kuma tallar kwayar da aka samo mai ‘karfi’. Daga nan idan ba a yi sa’a ba, sai ka ga idan matan suna da ’ya’ya, sai ka ga ’ya’yan sun zama ’yan aike, wanda daga hakan sai su koya musu shan kwaya. Na san wata yarinya da ba wuce shekara 7 ba, amma ta san sunayen kwayoyin da ake sha, wanda hakan ya samu asali ne daga aikenta da ake yi.

Don haka ne nake kira zuwa ga magidanta da su rika lura da yanayin gidansu, da halin da gida ke ciki. Idan matarka ba tad a lafiya, hakkinka ne ka kai ta asibiti a duba lafiyarta, sannan a rubuta muku magani.

Sannan ko da kuwa ba ku je asibiti ba, idan ka ga matarka na shan kwayoyi da yawa, to ya kamata ka garzaya zuwa wajen wani masani a bangaren domin yam aka bayani a kan kwayoyin.

Sannan kuma wannan matsalar tana da nasaba da rashin kula tare da sauke nauyin da Allah Ya daura wa wasu mazan. A wasu lokutan, mata da dama suna shiga cikin matsalar auratayya, da matsalar takan musu yawan gaske. Wata mata ta fada min cewa da ta je wajen boka ya mata ‘aiki’ a kan mijinta ya daina sat a cikin damuwa, gara ta sha kwayoyin kawai ta ‘dauke wuta’ a duk lokacin da mijin nata ya sanya ta cikin damuwa.

Don haka maza su sani cewa lallai idan matarka ta shiga irin wannan hali, kaima akwai na ka laifin, kuma Allah sai Ya kama ka. Kuma ba wai ina nufin mata su rika shiga irin wannan halin ba ne domin Allah zai kama mazan. Mu sani cewa ba a gyara barna da barna, ya kamata ne mu gyara barna da daidai.

Shawarata ga mata ita ce a duk lokacin da muka shiga matsala, ko kuma ga Allah, mu yi addu’a domin Allah ne ke maganin komai.

Da yawan lokuta, mazan sukan tauye hakkin matansu, kuma cikin fushi sai matan su yi addu’ar da tsinuwa ga mazan. Kuma kasancewar mazon Allah ya fada mace Allah Yana karban addu’ar wanda aka zalunta, sai Allah Ya karbi addu’ar. Wannan ne ya sa sai ka ga abubuwa na ta tabarbarewa.

A nan shawarat ita ce idan har mijinki ya zalunce ki, maimakon ki tsine masa, ki masa addu’ar Allah Ya shirye shi, domin Allah Yana karbar addu’ar wanda aka zalunta. Idan kina yi masa addu’ar shiriya, sai ki ga abubuwa sun canja cikin sauri da sauki.

Sannan kuma mata mu guji miyagun kwaye masu kawo mana tarnaki a gidajenmu. Shan kwaya ba zai taba zama maganin wata matsala ba. Sai dai ya karo matsalar. Addu’a da neman sulhu ne kadai suke iya kawo maganin matsalolin ma’aurata.

Sannan mu sani, zaman lafiya ya fi zama dan sarki.

 

Daga Nusaiba Suleiman Muhammad. Barikin Kotoko, NDA Kaduna.