Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Sheikh Isa Waziri: Babban bango ya fadi

Sheikh Isa Waziri: Babban bango ya fadi

Marigayi Sheikh Isa WaziriRasuwar Wazirin Kano Sheikh Isa Waziri a ranar Juma’ar da ta gabata ta girgiza jama’ar Kano, musamman ma kasancewar ana cikin wata mai albarka na azumin Ramadan, watan da marigayin ya saba yin tafsirin Alkur’ani Mai girma a cikinsa. Marigayi Wazirin na Kano ya rasu yana da shekara 89 a duniya.
Rasuwar tasa ta haifar da babban gibi kasancewarsa daya daga cikin manyan masu yada adinin Musulunci kuma daya daga cikin manyan mutanen jihar da suka riga mu gidan gaskiya.
Baya ga rashin kasancewar rashinsa rashi ne na muhimmin malami mai wa’azi da fadakarwa, haka rashin Sheikh Isa Waziri rasa uba ne kuma dattijo sauran mazan-jiya da ake dogaro da shi wajen samun shawarwari da shiryarwa, a masarautar Kano, masarauta mafi yawan jama’a a kasar nan.
A bangaren shahararsa a fannin malanta kuwa, marigayin ya yi fice kuma ya yi suna a daukacin Jihar Kano da sauran sassan kasar nan, wajen yin wa’azi da tafsiri a cikin hikima da tattausar murya, tare kuma da fadar gaskiya ba tare da tsoro ko kunyar wani ba.
Salon tafsirin Sheikh Isa Waziri ya bambanta da na malamai da dama da suke maida hankali wajen sukar akidar wasu, ko sukar fahimta da masu mulki, inda ya fi mai da hankali wajen jan hankalin jama’a su yi aiki da abubuwan da Alkur’ani Mai girma yake koyawar a mu’amalarsu ta yau da kullum kamar gaskiya da rikon amana da cika alkawari da kula da Sallah da Azumi da Zakka da Hajji da sauransu.
Wannan salon wa’azi nasa ya sa ya shahara, musamman a shekarun 1980 zuwa 1990, inda musamman mata suka fi kaunar wa’azinsa da ake yada shi ta gidajen rediyo da talabijin.
Sheikh Isa Waziri wanda ya yi fama da rashin lafiya kafin ya rasu ne a ranar ta Juma’a da misalin karfe 4:00 na yamma, ya rasu ne a lokacin da ake kokarin kai shi asibiti don duba lafiyarsa, bayan da rashin lafiyar ta tsananta.
Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 24, maza 12 da mata 12, kuma ya bar jikoki kimanin 50.
Sheikh Isa Waziri ya fara karatun addini a wurin mahaifinsa Wazirin Kano Gidado, bayan rasuwarsa ya koma karatu wurin babban wansa tsohon Waziri Malam Cigari daga nan kuma ya koma karatu wurin wani wansa kuma tsohon Wazirin Kano Shehu Gidado. Daga nan ya shiga Makarantar Koyon Larabci ta Kano, kafin ya shiga Babbar Makarantar Ilimin Addinin Musulunci ta Shahuci da ke Kano.
Sheikh Isa Waziri ya tafi kasar Masar, inda ya yi karatu mai zurfi a fannin Tafsirin Alkur’ani da sauran fannonin addinin Musulunci, inda bayan dawowarsa daga Masar ya fara da aikin koyarwa kafin ya koma alkalanci, wanda ya kai shi zama a garuruwan Jihar Kano kamar su Minjibir da Gwarzo da Zakirai da sauransu.
Bayan ya bar alkalanci ne sai ya koma harkar koyarwa, inda ya zama Mataimakin Shugaban Kwalejin Koyon Larabci ta Gwale.
Sheikh Isa Waziri ya yi ritaya daga aiki a 1981, kuma a lokacin ne aka nada shi Limamin Masallacin Juma’a na Murtala Muhammad da ke Kano. Yana wannan matsayin ne ya rika yin Tafsirin da ya fito da shi ya shahara a wurin jama’ar Musulmin Kano da ma wasu jihohin kasar nan.
Yana Limamin Masallacin Murtala ne a shekarar 2000 aka nada shi Limamin Babban Masallacin Kano da ke kofar fadar Mai Martaba Sarkin Kano. Kuma a wannan shekarar ce aka nada shi Wazirin Kano, inda ya kasance Waziri na Takwas a jerin Waziran zuriyar Fulanin Gidadawa a Kano. Ya shafe shekara 13 yana rike Wazirin Kano kafin rasuwarsa.
An yi jana’izar marigayi Sheikh Isa Waziri a kofar Kudu da ke fadar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, inda aka binne shi a makabartar Gwauron Dutse da kimanin karfe 7:00 na yamma, a ranar Juma’ar da ta gabata.
Kasancewar Mai Martaba Sarkin  Kano ba ya kasar nan a lokacin rasuwar Sheikh Isa Waziri, wadanda suka sallace shi sun hada da Wamban Kano, Alhaji Abbas Sunusi da Limamin Kano, Farfesa Sani Zaharaddeen da Sheikh Tijjani Bala kalarawi da Sheikh Yusuf Ali da sauaran manyan mutane da dubban jama’ar gari.
Allah Ya rahamshe shi, Ya sa mu samu guzurin tarar da shi, kuma mu cika da imani, amin summa amin.