✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara 20 da rasuwar Shata: Abin da ya bambanta shi da sauran mawaka

Har yau ba ku samo canjina ba, Balle in ce zan huta in dan samu in sarara” – Alhaji Maman Shata a cikin Bakandamiyarsa.   …

Har yau ba ku samo canjina ba, Balle in ce zan huta in dan samu in sarara” – Alhaji Maman Shata a cikin Bakandamiyarsa.           

A ranar Talatar da ta gabata ce, aka gudanar da bikin cika shekara 20 cif da rasuwar shahararren mawakin na Hausa, Alhaji Mamman Shata, wanda ya bar duniya yana da shekara 77, a ranar 18 ga watan Yuni, 1999.

Aminiya ta gana da daya daga cikin marubuta tarihin marigayin Dokta Aliyu Ibrahim Kankara, kan abin da ya sani game da abin da ya bambanta Shata da sauran mawaka.

Dokta Aliyu ya ce a bakin bincikensa, babban abin da ya gano shi ne Shata ya sha bamban da sauran mawaka, kuma wannan bambanci ne ya hada shi fada da sauran mawaka da maroka. Ya ce Shata ya yi musu zarra ne, ta hanyar yin kyauta, bayan dauke kansa da ya yi daga cikinsu.

“Ma’ana, shi maroki kullum tunaninsa a ba shi, ba shi ya ba da ba. To shi Shata ba haka yake ba, domin sau da yawa sai ya je ya yi wasa ya samu kudi amma ya ga damar duk abin da ya samun zai rabar da shi nan ga sauran maroka da mawakan da suka zo wajen. Hatta da Sarkin Daura Bashar wanda yake shi ne ubangidansa amma Shata na yi masa kyauta, musamman a lokutan Sallar Gani da wasu bukukuwa,” inji shi.

Ya ce “Abu na biyu shi ne, mutane na kallonsa a matsayin hatsabibi. To wannan hatsabibancin da ake kallo bai kai kashi daya bisa goman abin da mahaifinsa ke yi ba. Domin mahaifinsa maharbi ne wanda sai da ta kai fagen daga gidansa yake kira namun daji su zo, ya yi abin da zai yi, ya kora su su koma daji.”

Dokta Aliyu Kankara ya ce, akwai sadaukantaka da Allah Ya yi wa Shata, ta yadda zai yi abu ya kwana lafiya in wani ya yi ya samu matsala. “Dauki misalin jin muryarsa a wajen hira ko waka, in yana yi mutum na saurare bai so ya bari. Shata ne za a shiga yawon harbi a cikin daji wanda ana iya yin kwana uku ko fiye amma har a dawo gida ba za ku ji ya ce yana jin yunwa ba. Shata ne zai nuna Basaraken da ya kasaita da yatsa ya gaya masa duk maganar da ya ga dama, karshe ma ya ambace shi da yaro, amma babu abin da zai faru,” inji shi.

 Marigayi Ja’e Dan Ali daya daga cikin wadanda Shata ya waqe tare da matansa, Janjan da Mulasa
Marigayi Ja’e Dan Ali daya daga cikin wadanda Shata ya waqe tare da matansa, Janjan da Mulasa

Ko Shata ya taba mayar da kyautar da aka yi masa?

Dokta Kankara ya amsa da cewa “Muddaha Danraka ya taba yi masa kyautar mota sabuwa amma ya ce a mayar ba ya so saboda ba a hado ta da tukwici (kudin mai) ba. Hakan aka yi, aka mayar da motar Zariya, Danraka ya bayar da kudi masu yawa aka dawo masa sannan ya amsa. Kazalika, marigayi Dankabo ya ba shi mota ya ce bai gode ba, amma an dauki wannan a cikin raha ne aka yi. Har ila yau, akwai kyautar da aka yi masa wadda har ya mutu bai manta da ita ba, ita ce kyautar matar aure wadda Dagacin Falgore Alhaji Sani ya yi masa.”

“A da da mahaifinsa Sanin, Alhaji Bello suke abin arziki da Shata, to bayan rasuwarsa abin ya dawo ga dan wato Alhaji Sani. Wata rana ce suna zaune a Gozaki suna hira, sai  Shatan ya ce, mene ne za ka yi mini yadda amincinmu zai dore har abada? Shi kuma ya ce ya ba shi ’yarsa. Karshe dai har Shatan ya je wajen daurin auren amma kuma bai san da shi aka daura ba sai lokacin da aka zo ana jaddada masa cewa sai ya yi hakuri saboda akwai yarinta a wajenta. Wannan kyauta ta amarya Dije, Shata har ya bar duniya yana tunata,” inji Kankara.

A lokacin da Shata ke raye kuma har zuwa yau, akwai wadanda suke hasashen cewa asiri ba ya kama shi. To amma yaya gaskiyar wannan batu? Dokta Kankara ya kawo misalan wasu asirce-asircen da ake zargin an yi masa. “Akwai wanda aka hada baki da yaronsa mai suna Dangaude, inda ya sato wani rataye da wani ya yi wa Shatan don kariya saboda wata rashin lafiyar da ya taba yi. Wani mai kudi ya sa Dangaude ya sato masa. Bayan ya sato ya kawo masa, shi kuma ya toya ratayen amma kuma shi Dangauden bai kwana duniya ba a wannan rana. Shi kuma mai kudin idanunsa suka tsiyaye. Sannan akwai wani asiri wanda Dodo Karofi mai kidin Asawwara ya yi wa Shatan, hadin baki da wadansu inda ya yi tsawon wata 6 yana bin Shata don kawai ya debi kasar sawun kafarsa da gashin goshinsa. Ya kuma samu nasara wanda har sai da Shata ya yi shekara guda ba ya da lafiya. Amma a karshe Wadayi ya ba shi maganin da ya warke kuma tun daga wannan lokacin asirin bai kara kama shi ba har ya bar duniya.”

Dangane da batun wakokinsa kuwa, binciken Aminiya ya gano cewa Shata ne kadai ke sarrafa waka daya ya yi ta gida-gida. Misali, Bakandamiya, sai da ya sarrafa ta har sama da nau’i 100. A nan ya yi kari, can ya sanya wani ko wadansu, ko kuma ya yi wa kansa shi kadai. Kuma ita wakar da ya yi ta Tauhidi tare da addu’o’i, wadanda Allah Ya amsa masa dukkan addu’o’in da ya yi a cikinta a wajen karshen rayuwarsa, inda Allah Ya hada shi da Dankabo. Haka kuma bayani ya tabbata cewa kafin rasuwarsa ya yi nadamar wasu wakokinsa kuma har ya rasu ba ya son jin su, wato wakokin ‘Gagarabadau’ da ‘Hassan na Usaini’ da kuma ‘Muna Ji Muna Gani.’

Alhaji Ibrahim Danmadamin Birnin Magaji masani ne kuma mai sharhi kan wakokin Hausa. Aminiya ta tuntube shi kan ko yaya yake kallon shu’umancin Shata? Ya ce shi abin mamakin da aka ce Shatan na da shi shi ne ya gani ba shu’umanci ba. “Ba zan manta lokacin da na taba zuwa yin hira da shi ba a gidansa, duk wasu abubuwan da aka rika gaya mana kafin mu je, zuwan namu na ga ba haka ba ne. Shata mutum ne mai son yin raha da wasa da dariya. Kuma mutum ne mai hakuri, ya kuma iya tafiyar da kowa a yadda ya same shi. Kusan babu tambayar da bai amsa mini ba a matsayina na dan jarida. Abu daya ne kawai na lura da shi game da rayuwarsa, wato ba ya son raini,” inji shi.

Shi kuwa Injiniya Muttaka Rabe Darma bayyana Shata ya yi a matsayin mai falsafa, wanda babu inda bai tabo ba a wakokinsa da suka shafi rayuwar mutane da dabbobi da tsuntsaye hatta da yanayi.

Alhaji Amadu Na-Funtuwa Sa’in Katsina, babban abokin Shata ne, ya bayyana yadda Shata ya fara waka. “Ko da can da ake cewa yana tallar goro ne ya fara waka, a lokacin ba waka ce yake yi ba. Shi dan rawa ne kuma an sanya shi yin rawar da wata yarinya mai suna Indon Dutsen Reme a garin Bakori.”

Ko wane ne ya gaji Shata a cikin ’ya’yan da ya bari? Aminiya ta gana da daya daga cikin ’ya’yan marigayin, Sanusi Mamman Shata, wanda a yanzu yake ta kokarin gadon mahaifin nasu ta fuskar waka. Ya ce, “Mu babu abin da za mu ce sai godiya ga Allah da kuma jama’ar da har gobe suke tunawa da mahaifinmu kan irin gudunmawar da ya ba da duk kuwa da kasancewa ta fuskar waka ce. Lallai mahaifinmu ya taka muhimmiyar rawa ga al’umma. Muna ci gaba da yi masa addu’a kuma in Allah Ya so za mu ci gaba daga inda ya tsaya,” inji shi.