✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shekara guda: Har yanzu Fintiri bai yi wa Adamawa aiki ba – APC

Shekara guda da hawansa mulki har yanzu Gwamnan Adamawa bai kammala aiki ko daya ba, a cewar jam’iyyar APC. Jam’iyyar na kuma zargin Gwama Umaru…

Shekara guda da hawansa mulki har yanzu Gwamnan Adamawa bai kammala aiki ko daya ba, a cewar jam’iyyar APC.

Jam’iyyar na kuma zargin Gwama Umaru Fintiri na jam’iyyar PDP da kasa kaddamar da ko da aiki daya a jihar.

Skataren APC reshen jihar Adamawa Wafanri Theman ya ce saboda haka shekara daya na gwamnatin PDP  bata lokaci ne a jihar.

APC ta kuma ce mulkin PDP suna ne  jihar saboda tafiyar hawainiyarta wurin gudanar da ayyuka sabanin gwamnatin APC.

“Dukkanmu mun ga abin da APC ta yi a baya amma PDP ta ba da kunya.

“Mutane sun so su ga bambanci wurin samun cigaba amma gwamnatin nan ba ta himma”, inji shi.

Ya ce APC ta shugabanci jihar a lokacin matsin tattalin arziki amma duk da haka a shekaranta na farko ta yi manyan ayyuka.

Don haka a cewarsa PDP mai ci a yanzu ba ta da hujjar kasa kammala ko aiki daya a shekara guda na mulkinta.

A martaninsa, Gwamna Umaru Fintiri ya ce batun kammalam ayyuka ba matsalar jam’iyyar APC ba ce.

Ya kara da cewa gwamantin PDP a jihar ba ta sayar da kwangiloli yadda ya zargi APC da yi a baya.

Gwamnan ya ce ayyukan da gwamantinsa ke yi manya ne masu wa’adi mai tsawo kammlawa.

Gwamnan ya ce ayyukan cigaba ba su takaita ga gine-gine ba kawai, sun shafi kyautata rayuwar jama’a.

A cewarsa iyalai sun shaida ayyukan cigaban gwamnatinsa ta hanyar samun tallafin naira 15,000 zuwa 30,000.

“Ba aikinsu ba ne bayan sun kasa su je suna surutai a kan matsalar da ba ta shafe su ba, inji gwamnan.