✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shigar badala: An dakatar da Nafisa Abdullahi shekara biyu *An yi wa Fati Washa da Ummi Lollipop afuwa

A ranar Litinin da ta gabata ne Kwamitin Gyara Kayanka da ke karkashin kungiyar Fina-finan Hausa ta Arewa Film Makers da kuma MOPPAN ya dakatar…

A ranar Litinin da ta gabata ne Kwamitin Gyara Kayanka da ke karkashin kungiyar Fina-finan Hausa ta Arewa Film Makers da kuma MOPPAN ya dakatar da Jaruma Nafisa Abdullahi fitowa a fim har tsawon shekara biyu bisa laifin kin amsa gayyatar kwamitin da bayan ya tuhume ta da shigar badala da kuma shirya shagulgula (parties).
Kwimitin ya yi wa Fati Washa da Ummi Lollipop afuwa bayan sun amsar gayyatarsa sun kuma amince da laifuffukan da aka tuhume su har suka rubuta takardar ba da hakuri.
Kwamitin ya gayyacin ‘yan fim da suka hada da Nafisa Abdullahi da Fati Washa da kuma Ummi Lollipop bisa ga shigar badala da suka yi a lokutan mabambanta da kuma shirya/halartar shagulgula (party) da suka yi.
 Shugaban kungiyar ‘yan fim ta Arewa Film Makers, Isma’il Afakallah wanda kuma mamba ne a cikin kwamitin gyara kayanka ya yi wa wakilinmu bayanin yadda zaman ya kasance da kuma hukunci da yanke wa jaruman.
Ya ce: “Mukam gayyacin ‘yan fim ne a duk lokacin da muka ga wani al’amari ya taso da zai iya haifar da matsala ga al’umma ko masana’antar fim, sai mu kira su mu ladaftar da na ladaftarwa ko kuma mu ja kunnen wadanda ya kamata a ja kunnensu. Hakan ne ya sanya muka gayyaci Ummi Lollipop da Nafisa Abdullahi da kuma Fati Washa ofishin kungiyar Arewa Film Makers don su kare kansu. An yi zaman ne a karkashin kungiyar Arewa Film Makers da MOPPAN da sauran kungiyoyin da suka shafi harkar fim. Fati Washa da Ummi sun halarci zaman, an kuma karanta musu laifuffukan da ake tuhumarsu da aikatawa, wato shigar badala da kuma halarta shagulgulan da ba su dace ba, sun amince tare da rubuta takardar ba da hakuri hade daukar alkawarin ba za su sake aikata hakan ba. Daga nan muka shaida musu cewa su (‘yan fim) madubi ne ga al’umma, bai kamata su rika yin hakan ba, domin duk abin da suka aikata za a rika koyi da su. A yanzu kungiyar Arewa ta yi musu afuwa.”
A bangaren Nafisa kuma Afakalla ya ce, Nafisa ba ta halarci zaman ba, amma sai wani ya ce shi ne wakilinta, kwamiti ya nemi mutumin ya kira Nafisa don ta tabbatar shi wakilinta ne, sannan ya sanya a fili kowa ya ji, bayan ya kira ta ne sai jarumar ta ce ba ta turo wani wakili ba. Ko da kwamitin ya tambayi dalilin rashin zuwanta sai ta ce daga farko ta yi niyyar zuwa amma a wannan lokacin tana da wani abu mai mahimmanci da zai hana ta zuwa.
“Daga nan sai kwamiti ya yi zama sannan ya dakatar da ita fim na tsawon shekara biyu, kasancewar ta nuna babu wanda ya isa ya yi mata wani abu, ko kuma tafi karfin doka. A yanzu an fitar da takardar kuma za a raba ta ga Hukumar Tace Fina-finai ta kasa (National Censorship Board) da kuma Jiha.” Inji Afakallah
Tun da aka fara wannan batu akwai wadanda suka yi korafin ai jarumi Adam A Zango ya shirya shagali a kwanakin baya amma ba ku gayyace shi ba ko me za ka ce kan hakan? Sai ya ce: “Abin da nake so a fahimta shi ne duk abin da ka rufe kanka to shari’a ba ta binka ta yanke maka hukunci. Dangane da Zango ba mu da wata shaida da za ta nuna ya yi shagalin da ya kunshi shigar badala. Hasali ma labarin nake ji wai ya shirya shagali. Ba mu da hoto, ba mu da takaimaiman abin da za mu kama Zango da shi.  Dangane da Nafisa kuwa muna da kwararan shaidu a kanta. Idan da a ce ta killace kanta a wani wuri babu abin da ya shafe mu da ita. Ina so a fahimci rayuwar wanda ya yi suna (celebrity) daban take, duk lokacin da ya yi abu kwaikwayo ake yi. A lura ba wai muna da wani abu a kan Nafisa ba ne, ko a baya mun ladaftar da Safiya Musa da Maryam Malika da sauransu.”
Kwamitin Gyara Kayanka ya hada da Alhaji Abdullahi Sani Abdullahi Baba karami (Shugaba) da Mahmud Daneji Tantiri (Sakatare) da Dattawa guda biyu Shugaba kungiyar MOPPAN ta jiha  Khalid Musa da Kamilu Muhammad Jigon Hausa. Sauran mambobin  kwamitin sun hada da Isma’ila Afakalla da Misbahu M Ahmad da Falalu dorayi da kuma Yaseen Auwal.