Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Shinkafar da ake shigowa da ita na dauke da guba- Kwastam

Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya Kanar Hameed Ali ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina amfani da shinkafar da ake shigowa da ita daga kasashen waje saboda tana dauke da guba a ciki.

Shugaban ya bayyana hakan ne yau a Abuja a wani taron manema manema labarai da ma’aikatar kudi ta shirya

ADVERTISEMENT

Kanar Hameed Ali ya ce, Gwamnatin tarayya ba ta baiwa wasu lasisin shigowa da shinkafa cikin Najeriya ba don haka duk shinkafar waje da take yaduwa a cikin kasar an yi safarar ta ne. Don haka shinkafar da ake shigowa da ita tana dauke da guba, akalla shinkafar sai da ta yi shekara biyar a ajiye kafin a shigo da ita cikin Najeriya.

ADVERTISEMENT