Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Shinkafar lambu da miyar kaza

Shinkafar lambu da miyar kaza

Assalamu alaikum uwargida tare da fatar alheri kuma ana cikin koshin lafiya. Tare da fatar an yi Sallah lafiya. Kamar yadda nake fada a kullum akwai hanyoyi da dama da ake bi don girka abinci daban-daban kuma akwai hanyoyi da dama wadannda ake bi don girka shinkafa walau dafa-duka ko fara ko kuma ta lambu. Yana da kyau a koyi nau’o’in girke-girke domin yi wa baki da manyan gobe. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da za a bukata

  • Shinkafa
  • Karas
  • Koren wake
  • ‘Peas’

Hadi              

A samu shinkafa a yi mata tafasar farko sai a wanke a tsame ta. Sannan a kankare karas a yayyanka shi kanana sannan a samu koren wake a wanke sai a yayyanka kanana a sake ajiyewa a gefe. A samu peas a wanke sai a ajiye a gefe.

A sake zuba wani ruwan zafi a wuta bayan ya tafasa sai a zuba shinkafar da yankakken karas da koren wake da peas su dahu tare.

A wanke kaza sai a tafasa da albasa da gishiri da thyme. Bayan ya silalu yayi laushi, sai a sake yanka wani albasa da tumatir da attarugu. A fara soya albasa sannan tumatir da attarugun. Idan sun soyu, sai a zuba magi da kori da garin tafarnuwa kadan.

A dauko wannan silalen naman kazan a zuba da dan romo kadan domin inganta miyar. Hmmn! Lagwada!

Za a iya hada wannan girkin da sauce din kaza ko na koda.