Da Dumi Dumi

Shirin tsaro na Amotekun na samun goyon bayan sarakunan Yarbawa

Shirin samar da tsaro na ‘Amotekun’ wadda da Yarbanci ke nufin Damisa don samar da dakaru na musamman da suka hada jami’an tsaro da maharba da mafarauta da ’ya’yan Kungiyar OPC a jihohin Yarbawa da aka kaddamar a jiya Alhamis bayan taron neman mafita ga kalubalen tsaro  da gwamnonin jihohin Kudu maso Yamma suka yi a garin Ibadan da ke jihar Oyo a karshen bara da suka ce shiri ne da zai taimaka wajen kyautatuwar tsaro a yankin yana samun goyon bayan sarakunan yankin.

A Jihar Ogun babban basaraken kasar Egba, Oba Adedotun Gbadebo, ya bayyana goyon bayansa ga shirin na Amotekun, inda ya ce shiri ne da zai dafa wa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu na tsare dukiyoyi da rayukan al’ummar yankin.

A zantawarsa da manema labarai Alake na kasar Egba, ya ce duk wani shiri na dafa wa jami’an tsaro da bai saba ka’ida ba, bai kuma yi hannun riga da dokar kasa ba, abu ne da ya kamata a ba shi goyon baya. Don haka ya bayyana goyon bayansa ga shirin samar da tsaro a yankin Kudu maso Yamma na Amotekun.

Alake na kasar Egba, wanda tsohon soja ne kafin ya zama Basarake ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata lokacin da Mataimakin Sufeton Janar na ’Yan sandan Najeriya mai kula da Shiyya ta Biyu da ta hada da jihohin Legas da Ogun, Alhaji Ahmed Iliyasu ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa da ke Ake a birnin Abeokuta a Jihar Ogun.

A nasa bangaren Alhaji Ahmed Iliyasu ya shaida wa manema labarai cewa, hanyar tabbatar da tsaro da yaki da miyagun laifuffuka ita ce, gudanar da al’amuran tabbatar da tsaro tare da jama’a da kuma amfani da kimiyya da fasahar zamani wajen ayyukan tsaro, “Kamar yadda Sufeto Janar ’Yan sandan Najeriya, Alhaji Mohammed Adamu, ya zayyana ya kuma bada umarnin gudanar da ayyukan ’yan sanda ta hanyar amfani da fasahar zamani. Wannan shi ne turbar da za a bi wajen magance miyagun laifuka da tabbatar da tsaro,” inji shi.

ADVERTISEMENT

Alhaji Ahmed Iliyasu, ya shaida wa Aminiya cewa ya yi rangadi a Jihar Ogun ce a kokarin da rundunar ’yan sandan ke yi na ganin a kara tabbatar da tsaro a jihohin Legas da Ogun, inda ya ziyarci Gwamnan Jihar Ogun, Yarima Dapo Abiodun da Basaraken Kasar Egba da ’yan majalisarsa, ya kuma gana da kungiyoyin sa-kai da na kare hakkin dan Adam da na hulda a tsakanin ’yan sanda da jama’a (PCRC), kuma a karshe ya yi ganawar sirri da ’yan sandan jihar.

“Kamar yadda na shaida maka ne, aikin tsaro ana yin sa ne tare da jama’a wannan ne dalilin da ya sanya a koyaushe muke kyautata alakarmu da jama’ar yankin da muke aiki,” inji shi.

Alhaji Ahmed Iliyasu, ya shaida wa Aminiya cewa akwai kyawawan tsare- tsare na fasahar zamani da Babban Sufeton ’Yan sandan Najeriya Alhaji Mohammed Adamu ya bullo da su, “Don haka na yi wa jami’anmu albishir na kyawawan tsare- tsare da Babban Sufeton ya bullo da su, abubuwan da suka shafi aiki da fasahar zamani, kayan aiki da  sauransu wadanda za su taimaka wa jami’anmu a ayyukansu na tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a,” inji shi.

Kalubalen tsaro da ake fama da shi a sassan kasar nan musamman Arewa ne ya sanya shugabannin jihohin Kudu maso Yamma, suka yunkuro domin sama wa kansu mafita. Wannan ne ya sa suka kai ga kirkiro shirin Amotekun.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya