✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba Muhammad Mursi: Duniya ta yi asarar jan gwarzo

A makon da jiya, ranar Litinin, 17-06-2019 al’ummar Musulmi da duniyar mutanen kirki suka yi rashin jan gwarzo, tsohon Shugaban Kasar Masar, Muhammad Mursi. A…

A makon da jiya, ranar Litinin, 17-06-2019 al’ummar Musulmi da duniyar mutanen kirki suka yi rashin jan gwarzo, tsohon Shugaban Kasar Masar, Muhammad Mursi. A wannan makon, GIZAGO (08065576011) yana dauke da ta’aziyyar wannan muzakkarin shugaba, mai kishin al’ummarsa:

Muhammad Mursi: Shi ne Shugaba na farko da aka fara zaba a tsarin dimokuradiyya a kasar Masar. Amma abin mamaki, duk da cewa kasashen duniya suna tilasta wa kasashe bin tsarin na dimokuradiyya amma sai suka kasance ’yan kutungwila da tsugudidi, suka kitsa masa juyin mulki bayan shekara daya kacal da hawansa mulki.

Wane ne Mursi? Shi Balarabe ne kuma Musulmi mai tsananin kishin addininsa, masoyin Manzon Allah Muhammadu (SAW) ne na hakika, wanda duk inda ya samu wuri sai ya yi masa salati. An haife shi ne a 1951, a kauyen El-Adwah da ke gabar Kogin Nilu, a Lardin Sharkiyya a kasar Masar. Ya samu tarbiyyar karatu na addini da na zamani tun daga farkon rayuwarsa. Ya auri mata daya, wacce ta haifa masa ’ya’ya biyar – maza hudu da mace daya. Ya amsa kiran Allah yana da shekara 68, ya bar matarsa da ’ya’yansa da kuma dimbin masoya a fadin duniya.

Kamar yadda masana rayuwarsa suka tabbatar, Muhammad Mursi mutum ne mai son ilimi, mai kishin neman ilimi. Yana dan shekara 24 a duniya (1975) ya samu digirinsa na farko a fannin Injiniyan Karafa, sannan kuma a 1978 ya samu digirinsa na biyu, duk dai a wannan fannin daga Jami’ar Alkahira, Masar.

A karatun addini kuwa, marigayin masani ne na gaban sahu, tun yana saurayi, a  1983 yana dan shekara 32 a duniya ya haddace Alkur’ani Mai girma sannan ya ci gaba da karatu da neman ilimi babu kama hannun yaro.

A shekarar 2013 da Gwamnatin Alsisi ta kama shi ta tsare, babu abin da yake yi a cikin kurkuku, daga ibada sai tilawar Alkur’ani. An ruwaito cewa ya nemi masu tsaronsa su ba shi Alkur’ani ya kasance tare da shi amma suka ki. Shi ne ya bayyana cewa:

“Sun ki su ba ni Alkur’ani. Ba ina son karanta shi ba ne, domin kuwa na haddace shi shekara talatin da suka wuce. Ina son in rika shafa shi ne kawai.”

Marigayin ba kifin rijiya ba ne, domin kuwa ya shiga duniya, ya samu ilimin mu’amala da mabambantan mutanen duniya,  a 1982 ya tafi Amurka, inda ya yi digirinsa na uku a Jami’ar Kalifoniya ta Kudu. Ya yi zaman Amurka na tsawon shekara uku, inda ya dawo kasarsa a 1985.

Saboda kishinsa na yi wa al’umma hidima, ya shiga cikin kungiyar ’Yan uwa Musulmi (Ikhwanu) a 1977, inda ya rike mukamai da dama a cikin kungiyar. Haka kuma ya shiga siyasa kai-tsaye, inda ya ci gaba da gwagwarmaya. Ya yi takarar mukamai daban-daban a lokuta da dama a matakin Majalisar Kasa. Ya zama Dan Majalisa a shekarar 2000.

A lokacin da ya kammala karatunsa a Amurka, ba wani abu ne ya sanya ya dawo Masar ba, sai kishirwarsa ta yi wa al’ummarsa hidima. Don haka bayan dawowarsa, ya yi aikin koyarwa a Jami’ar Zakazik ta kasar Masar daga 1985 zuwa shekarar 2010. Shi ne ma ya shugabanci Tsangayar Koyar da Injiniyancin Karafa ta Jami’ar.

Saboda ganin dacewarsa da salonsa na iya jagoranci da tausayin al’ummarsa da kishin addinisa, sai kungiyarsa ta ’Yan uwa Musulmi ta tsaida shi a matsayin dan takarar Shugaban Kasa, inda aka kara tsakanin manyan ’yan takara guda biyar a kasar bayan boren da ya yi awon gaba da Shugaba Hosni Mubarak a shekarar 2011.

Marigayi Mursi ya ci nasarar zama Shugaban Kasa na farko a dimokuradiyance bayan lashe zaben da ya yi da kashi 52 cikin 100, inda ya kada babban abokin hamayyarsa, Ahmad Shafik a shekarar 2012. An bayyana cewa wannan shi ne zabe da ya zamo mafi tsabta a tarihin kasar Masar.

Shekara daya kacal ya yi a kan mulki, inda ya samu kauna ta ban mamaki daga al’ummar Larabawa da sauran Musulmin duniya, wadanda suka rika yi masa kallon jagoran da zai dawo musu da kimarsu a duniya, musamman yadda yake nuna damuwarsa da al’ummar Musulmi da yadda yake nuna goyon bayansa ga mutanen Palasdinu da Zirin Gaza.

Kamar yadda Sashen Hausa na BBC ya ruwaito, mutanen da suka yi adawa da shi, sun zarge shi da barin masu tsananin kishin Musulunci suna cin karensu ba babbaka a fagen siyasar kasar. Haka kuma sun dora masa laifin rashin iya tafiyar da tattalin arzikin kasar. Sai dai magoya bayansa da masu bibiyar al’amuran da ke gudana a Masar suka musanta wadannan zarge-zarge.

A lokacin da yake raye, shi da kansa ya yi zargin wadansu daga manyan kasashen duniya da iza wutar yi masa adawa. Dalili ke nan a daya daga cikin jawabansa ga al’ummar Masar, ya gargade su da cewa: “Kada ku hallaka zakokin kasarku, domin muddin kuka yi haka, to babu shakka karnukan makiyanku za su yi watanda da ku.”

Sai dai masu adawa da mulkinsa ba su ji wannan gargadi nasa ba, domin kuwa sun yi ta shirya zanga-zanga a titunan kasar lokacin bikin cika shekara daya da hawansa mulki, a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2013.

Cikin ’yan kwanaki bayan fara zanga-zangar, a ranar 3 ga watan Yuli na 2013, sojoji suka dakatar da kundin tsarin mulkin kasar, inda suka sanar da kafa wata Gwamnatin Rikon Kwarya kafin gudanar da sabon zabe.

A kan haka ne kuma sai sojojin suka kama Mursi, domin ya yi watsi da matakin hambarar da gwamnatinsa da suka yi. Ministan tsaronsa da ya nada, Abdulfattah Al-Sisi ne aka zarga da kitsa wannan juyin mulki.

Magoya bayan Mursi sun ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana ta nuna rashin amincewarsu da juyin mulkin da Sisi ya yi wa zababben shugabansu kuma yake ci gaba da tsare shi tare da wadansu dubban magoya bayansa da kashe wadansu da tilasta wa da dama daga cikinsu yin gudun hijira zuwa kasashen ketare.

Wani abin takaici shi ne, yadda aka yi ta samun labarun yadda aka rika uzzura masa a kurkuku, inda aka hana shi muhimman abubuwa da yake so a rayuwarsa. Hatta da ya nemi a ba shi kwafin Alkur’ani, hana shi aka yi. Haka kuma duk da cewa ya yi fama da rashin lafiya, amma an ki ba shi kulawa ta musamman.

Babban dan marigayin mai suna Ahmad Mursi, ya bayyana cewa an yi jana’izar mahaifinsa a makabartar Al-Wafaa Wa al-Amal da ke gabashin Alkahira, sannan sun yi masa wanka a asibitin da ke cikin kurkukun da ake tsare da shi, sannan suka sallace shi duk a cikin kurkukun. Ya ce tun bayan sanarwar rasuwar mahaifinsa suka nemi a ba su gawarsa, don su binne shi a asalin mahaifarsa amma sai hukumomi suka ki amincewa da hakan, sannan suka ce ita kanta gawar Mursi mallakarsu ce, ba za su amince a binne shi a wajen iyalansa ba.

Wani abin mamaki shi ne, a ranar 17-6-2012 al’ummar Masar suka zabe shi a matsayin Shugaban Kasa kuma sai ga shi ya rasu a ranar 17-06-2019, a gaban kotun da ake yi masa shari’a.

Muhammad Mursi bai yi mutuwar banza ba, domin kuwa al’ummar duniya sun nuna masa kauna, suna cikin yi masa addu’a bisa zaluncin da aka yi masa.

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana shi a matsayin shahidi, sannan ya ce jininsa na kan Gwamnatin Masar. Mazauna birnin Istanbul sun yi masa Sallar Janaza, haka ma sauran kasashen Musulmi daban-daban sun yi irin wannan Sallah ga marigayin.

Allah Ya jikansa da rahama, amin!