Da Dumi Dumi

Shugaban Majalisar Jihar Edo ne ya kamu da Coronavirus

Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Edo Frank Okiye ne mutumin da aka tabbatar yana dauke da Coronavirus a jihar.

Mataimakin Gwamnan Jihar Philip Shaibu ne ya sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai bayan taron wani kwamiti da aka kaddamar don yaki da cutar.

“Okiye ya je Birtaniya ne amma bayan ya dawo ya killace kansa, da aka yi gwaji kuma sai aka gano yana dauke da cutar”, inji Mista Shaibu.

Sai dai gwajin da aka yi wa matar Shugaban Majalisar da ‘yarsa ya nuna ba su kamu da cutar ba.

Ranar Litinin ne dai hukumomin lafiya a Najeriya suka sanar da cewa an samu wani mai dauke da cutar a Jihar ta Edo.

ADVERTISEMENT
Sharing
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya