✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban Masar zai ci gaba da mulki har zuwa 2030

Majalisar Masar ta amince da gyara kundin tsarin mulkin kasar wanda zai ba Shugaban Kasar Abdul Fattah al-Sisi damar ci gaba da mulki har zuwa…

Majalisar Masar ta amince da gyara kundin tsarin mulkin kasar wanda zai ba Shugaban Kasar Abdul Fattah al-Sisi damar ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2030.

A shelarar 2022 ce ya kamata Sisi ya sauka bayan kawo karshen wa’adin mulkinsa. Amma sauya kundin mulkin wanda za a tabbatar a kuri’ar raba-gardama cikin kwanaki 30, zai tsawaita wa’adin mulkin zuwa shekara shida sannan ya kara ba shi damar sake tsayawa takara.

Kuma an kara wa Sisi karfin iko kan bangaren shari’a.

A shekarar 2013 ne Sisi a lokacin yana soja ya hambarar da gwamnatin farko da aka taba zaba a Masar ta Mohamed Morsi bayan zanga-zangar kin jinin gwamnatin.

Tun hawansa, an tsare dubban mutane tare da yanke wa wadansu da dama hukuncin kisa kamar yadda BBC ya ruwaito.

An zabi Sisi a matsayin Shugaban Kasa a shekarar 2014 sannan aka sake zabensa a bara bayan lashe kuri’u da kashi 97.

Babu wata adawa da ya fuskanta bayan manyan ’yan siyasa sun janye ko kuma an kama su.

Magoya bayan Al Sisi ne suka mamaye majalisar Masar, wacce ’yan adawa suka kira ’yan amshin shantansa.