✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban NDIC na Najeriya ya zama shugaban IADI na Afirka

A ranar Talatar da ta gabata ce aka zabi Babban Daraktan Hukumar NDIC na Najeriya, Umaru Ibrahim a matsayin sabon Shugaban Nahiyar Afirka a Hukumar…

A ranar Talatar da ta gabata ce aka zabi Babban Daraktan Hukumar NDIC na Najeriya, Umaru Ibrahim a matsayin sabon Shugaban Nahiyar Afirka a Hukumar IADI, yayin babban taron shekara-shekara da hukumomin ARC tare da hadin gwiwar IADI suka shirya a Legas.

A wata sanarwa da Shugaban Sashen Sadarwa da Watsa Labarai na Hukumar NDIC, Mohammed Kudu Ibrahim ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa zaben Umaru Ibrahim ya zo bayan da kusoshin hukumomin suka amince da nadin nasa sakamakon karewar wa’adin tsohon Shugaban, Mista John Chikura na kasar Zimbabwe.

Haka kuma taron ya zabi Mohamud A. Mohammed, Babban Daraktan Hukumar KDIC na kasar Kenya a matsayin Mataimakin Shugaban Afirka na Hukumar IADI.

Bugu da kari zaben Umaru Ibrahim din ya sake bai wa Najeriya damar yin shugabancin a karo na biyu, lokacin da hukumar ta zabi tsohon Babban Daraktan NDIC, Alhaji Ganiyu Ogunleye a matsayin shugaba na Afirka shekarun baya.