✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaban ‘yan Kungiyar asiri da ake nema ya shiga hannu

Rundunar ‘yan sandan Legas ta yi nasarar kame wani shugaban ‘yan Kungiyar asiri da ake nema ruwa a jallo Shugaban ‘yan kungiyar asirin mai suna Yusuf Omidele…

Rundunar ‘yan sandan Legas ta yi nasarar kame wani shugaban ‘yan Kungiyar asiri da ake nema ruwa a jallo

Shugaban ‘yan kungiyar asirin mai suna Yusuf Omidele wanda rundunar ‘yan sandan ta dade tana nema ruwa a jallo zai gurfana a gaban kotu, a lokuta da dama inda ya kare zaman kason sa na karshe a shekarar 2014

A wata sanar wa da kakakin rundunar ‘yan sandan Legas ya fitar DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa, rundunar ta kame wanda ake zargin wanda yake jagorantar kungiyar asiri ta Eiye tare da manbobin kungiyar asiri 20 wadanda suka hadar da na kungiyar da na abokiyar karawar su ta Aye. Ya ce, an kama su ne a lokacin da suke bata kashi da juna lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 2 tare da jikata mutum 6, ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar CP Zubairu Ma’azu, ya shirya zama na musamman tare da masu ruwa da tsaki domin kawo karshen miyagun ayyukan ‘yan kungiyar asiri a yankin Ikurodu dama sauran sassan jihar.