Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Shugabancin Majalisa: Gwamnonin APC sun amince da Lawan, Gbajabiamila

Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, ya ce tsofaffin Gwamnoni da suke majalisar dokokin tarayya sun amince da Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda zai jagoranci majalisar dattawa.

Gwamna Kashim ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin N’Djamena da ke kasar Chadi, ya kuma ce zababbun Sanatoci  sun amince da zabar Femi Gbajabiamila a matsayin kakakin majalisar wakilai.

ADVERTISEMENT

Gwamnan Bornon ya kara da cewa, duk zababbun Sanatoci da zababbun `yan majalisar wakilan tarayya daga jihar Borno suna goyon bayan shugabancin Lawan da Gbajabiamila.

ADVERTISEMENT