✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin APC sun janye dakatarwar da suka yi wa Oshiomhole

Shugabannin jam’iyyar APC na mazaba sun janye dakatarwar da suka yi wa shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole, wanda ya yi sanadiyyar barinsa kujerar. Mutum…

Shugabannin jam’iyyar APC na mazaba sun janye dakatarwar da suka yi wa shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole, wanda ya yi sanadiyyar barinsa kujerar.

Mutum 17 daga cikin ‘yan Kwamitin Zartarwar jam’iyyar na Mazaba ta 10 a Karamar Hukumar Etsako ta Yamma a jihar Edo sun rattaba hannu cewa sun janye dakatarwar da suka yi wa Oshiomhole.

Sun kuma bukaci shugabannin jam’iyyar a dukkan matakai da su dawo da shi kujerarsa ta Shugaban jam’iyyar na kasa.

A ranar Laraba ne dai Oshiomhole ya bar kujerar tasa bayan Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta tabbatar da hukuncin dakatarwar da Babban Kotu ta yi masa tun da farko.