✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin duniya sun cimma matsaya kan rikicin Libya

Shugabannin kasashen duniya sun amince a farkon mako su mutunta shirin haramta makamai da kuma janyewa daga Libya, inda gwamnatoci masu gaba da juna ke…

Shugabannin kasashen duniya sun amince a farkon mako su mutunta shirin haramta makamai da kuma janyewa daga Libya, inda gwamnatoci masu gaba da juna ke yakin neman iko.

Shugabannin kasashe 12 da manyan wakilai daga Kungiyoyin Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kungiyar Kasashen Larabawa sun gudanar da taron koli na wuni guda a birnin Berlin na kasar Jamus.

“Mun iya samun amincewar kowa cewa akwai bukatar mutunta yarjejeniyar haramta amfani da makamai  kuma a tsaurara aiwatar da wannan matsayar kamar yadda aka yi a baya,” inji Shugabar Jamus Angela Merkel mai masaukin baki a  jawabin bayan taro.

Ta ce haka batun yake kuma tana ganin abubuwan da suka faru a kwanakin baya sun isa shaidar cewa ayyukan soji ba su ne mafita ba, sai dai kara jefa mutane cikin wahala.

Mahalarta taron kolin sun amince da yarjejeniyar mako daya ta tsagaita wuta a Libya.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce akwai bukatar dukkan bangarorin su kara matsin lamba a kan masu gaba da juna a Libya, ganin cewa kasashe da dama na mara wa bangarori daban-daban na Libya baya.

Akwai damuwar Libya ka iya fadawa cikin halin da Syria ta tsinci kanta a ciki.