✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugabannin Jam’iyyar PDP sun shiga rudani a Jigawa

Shugabannin Jam’iyyar PDP a Jihar Jigawa sun shiga cikin rudani sakamakon bazuwar jita-jita cewa Gwamnatin Tarayya za ta tura kantoman da zai rike jam’iyyar a…

Shugabannin Jam’iyyar PDP a Jihar Jigawa sun shiga cikin rudani sakamakon bazuwar jita-jita cewa Gwamnatin Tarayya za ta tura kantoman da zai rike jam’iyyar a jihar lamarin da ya sa shugabannin kiran taron gaggawa a hedkwatar jam’iyyar.
 Taron wanda ya gudana a cikin sirri, shugabannin sun ki bayyana wa manema labarai dalilan kiransa.
Kwanakin baya ne tsohon Kwamashinan Ilimi na Jihar ya ce ana shirin kwace jam’iyyar daga hannun Gwamnan Jihar Jigawa saboda Shugaba Jonatthan bai aminta da take-taken Gwamna Sule Lamido ba, kuma hakan ana jin shi ya sa shugabaninin jam’iyyar suka kulle kansu daga safiyar shekaranjiya Laraba har zuwa La’asar a ofishin jam’iyyar suna ganawa.
Wata majiya mai tushe ta shaidaw a wakilimmu cewa kashi biyu cikin uku na ’yan Majalisar Jihar Jigawa sun fara shirin yi wa Gwamna Lamido tawaye domin tsira da kujerunsu.
Haka kwamashinonin jihar masu sha’awar tsayawa takarar majalisar jihar ko ta tarayya sun fara kai caffa ga tsohon Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Saminu Turaki saboda sun fara fahimtar cewa akwai yiwuwar Gwamnatin Tarayya ta kwace jagorancin jam’iyyar daga hannun Gwamna Lamido.
Bayanai sun nuna cewa wasu jiga-jigan gwamnatin jihar sun tare a Abuja domin neman yadda za a yi a daidaita tsakanin gwamnatin jihar da ta tarayya.
Da take magana a kan lamarin Shugabar Mata ta Jam’iyyar PDP ta Jihar Hajiya Talle Hadeja ta ce babu wani batun kwace jam’iyyar daga hannunsu. Ta ce batun taronsu a hedikwatar jam’iyyar ba sabon
al’amari ba ne, abu ne da suka saba yi duk wata don tattauna matsalolin jam’iyyar.
Ta ce akwai bukatar manema labarai su guji yada jita-jita marar ma’ana domin dadada wa wasu mutane, inda ta ce maganar da Alhaji Abba Anas yake yi cewa za a kwace jam’iyyar daga hannun mukarraban Gwamna Lamido babu kanshin gaskiya a cikinta.