Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Shugabannin kananan hukumomi sun yaba wa gwamnati kan ba su kudadensu kai-tsaye

Shugaban Karamar Hukumar Kaura da ke Jihar Kaduna Dokta Bege Ayuba Katuka da takwaransa na Karamar Hukumar Jama’a, Peter Danjuma Averik sun jinjina wa Gwamnatin Tarayya, kan ba su kudadensu kai tsaye daga Asusun Tarayya tare da yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna kan sake musu kudaden don ba su damar gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansu cikin sauki.

Shugaban Karamar Hukumar Kaura Dokta Bege Ayuba Katuka ya yi yabon ne a dakin taro na Karamar Hukumarsa ranar Juma’ar da ta gabata yayin gudanar da bikin cika shekara daya da kasancewa Shugaban Karamar Hukumar, inda ya ce wannan yunkuri na gwamnatin APC a karkashin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na bai wa kananan hukumomi damar cin gashin kansu shi ne babban romon da dimokuradiyya ta samar tun bayan dawowar mulkin farar hula.

ADVERTISEMENT

Ya ce wannan yunkuri zai ba da damar matso da gwamnati kusa da talakawa kasancewar karamar hukuma ce mafi kusa da jama’a musamman mazauna karkara.

“Babban aikinmu shi ne kirkiro da ayyukan da za su amfanar da dubban mutane mazauna karkara. Wannan na daga cikin alkawurran da wannan gwamnati ta yi wanda zai taimaka wajen samar da jin dadi da walwalar jama’a,” inji shi.

ADVERTISEMENT

A karshe ya yaba wa al’ummar karamar hukumar bisa goyon bayan da suke ba shi.

“Ban tara ku a nan don bayyana muku ayyukan da na yi ba, amma kowannenku shaida ne. Babban abin farin ciki da kuma kyautar da na samu shi ne yadda mutane za su taso daga kauyuka su ce mun gode da irin ayyukan da ka yi mana da suka hada da samar da gadoji da tsabtataccen ruwan sha da tsaro da kuma wutar lantarki,” inji shi.

Da suke tofa albarkacin bakinsu, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Mista Barnabas Bala Banted da Mataimakin Shugaban Ma’aikata a ofishin Mataimakiyar Gwamnan Jihar, Barista James Kanyip wadanda suka fito daga karamar hukumar sun yi kira ga jama’ar Kudancin Kaduna su daina yarda ana wasa da hankalinsu da sunan addini ko kabila ana barinsu a baya.

Sarakunan Marwa da Attakar da wakilin Sarkin Kagoro duka sun halarci taron.

Shi ma da yake nasa jawabin a wajen nasa bikin na cika shekara daya, Shugaban Karamar Hukumar Jama’a jinjina wa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da cewa shi ne wanda ya fara ba kananan hukumomin jihar kwarya-kwaryar cin gashin kai a wasu fannoni wanda hakan ya bada damar share fagen ba su cukakkiyar dama daga Gwamnatin Tarayya.

“Abubuwan da na yi wa jama’a alkawari tun bayan hawa shugabancin karamar hukumar su ne samar da tsaro da zaman lafiya wanda su za su bada damar gudanar da sauran ayyukan ci gaba da su ka biyo baya. Hakan ne ya sa muka kirkiro da kananan ofisoshin ’yan sanda a gundumomin Jaginda da Barde da kuma Bakin Kogi da Kogum.”

Da yake jawabi, dan Majalisar Wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Jama’a da Sanga wanda shi ne Shugaban Taro, Shehu Nicholas Garba, ya bayyana namijin kokarin da Shugaban Karamar Hukuma ya yi na irin ayyukan da ya gudanar tare da jan hankalin zavavvun ’yan siyasa da su rika tara mutane tare da bayyana musu irin ayyukan da suka gudanar.

A karshe ya bukaci Shugaban Karamar Hukumar da ya kara rage damtse wajen kara aiwatar da aikace-aikace musamman da yanzu za su fara samun kudadensu daga Asusun Gwamnatin Tarayya.

Daga cikin ayyukan da ya gudanar a Karamar Hukumar Jama’a sun hada da gina kwalbatoci a kowace daya daga cikin gunduma sha biyu a karamar hukumar da samar da injin wuta na tiransifoma a Unguwan Musa da Unguwan Baiya da Takau da Barde da kuma gyara makarantun firamari na Ambam da Unguwan Gwandara da sauran ayyuka.

Sarakunan da ke karkashin karamar hukumar da suka hada da Sarkin Kaninkon da na Kagoma da Godogodo da Nyenkpa da wakilin Sarkin Fantswam da kuma Sarkin Jama’a duka sun halarci taron.