✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Siyasa da siffofin Bayin Mai rahama

Masallacin NASFAT na Kasa da ke Abuja Fassarar Salihu Makera “Godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya siffanta wadansu daga cikin bayinSa da cewa bayin…

Masallacin NASFAT na Kasa da ke Abuja

Fassarar Salihu Makera

“Godiya ta tabbata ga Allah, Wanda Ya siffanta wadansu daga cikin bayinSa da cewa bayin Shi Mai rahama ne. Godiya ta tabbata ga Allah Mai rahama Mai jinkai. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai Yaka ba Ya da abokin tarayya a gare Shi, Mai rahama wanda Ya daidaita a kan Al’arshi. Kuma na shaida lallai Shugabanmu Masoyinmu Abin girmamawarmu Abin Koyinmu kuma Maulanmu Muhammad BawanSa ne kuma ManzonSa ne, shi ne Shugaban Bayin Mai rahama, wanda yake cewa “Masu yin rahama Mai rahama Yana yi musu rahama. Ya Ubangiji! Ka kara salati a gare shi da alayensa salatin da za ka san da mu a kanta.

Ya bayin Allah! Hudubarmu ta yau za ta bayani ne a kan Bayin Mai rahama da siffofinsu, musamman a wannan lokaci da ake fama da batutuwan siyasa da zabe. Ya bayin Allah! Wajibi ne a kan kowane Musulmi ya kasance mai kadaita Allah mumini muhsini, bawa ga Mai rahama, namiji ne ko mace babba ne ko yaro malami ne ko mai neman ilimi, dan kasa ne ko waninsa dan siyasa ne ko a’a ba bawan son ransa ba. Mai rahama (Allah SWT), Ya ce game da bayinSa a cikin Suratul Furkan aya ta 63 zuwa ta 76. “Kuma bayin Mai rahama su ne wadanda ke yin tafiya a kan kasa da sauki, kuma idan jahilai sun yi musu magana (ta bata rai ko takala), sai su ce, “Salama” (a zama lafiya). kuma (su ne) wadanda suke kwana suna masu sujua da tsayuwa ga Ubangijinsu. Kuma (su ne) wadanda suke cewa “Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azabar Jahannama daga gare mu. Lallai ne azabarta ta zama tara. Lallai ne ita ta munana ta zama wurin tabbata da mazauni. Kuma (su ne) wadanda suke idan sun ciyar ba su yin barna, kuma ba su yin kwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta ksance a tsakanin wancan da tsakaitawa. Kuma (su ne) wadanda ba su kiran wani ubangiji tare da Allah, kuma ba su kashe rai wanda Allah Ya haramta face da hakki, kuma ba su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan zai gamu da laifuffuka. A ribanya masa azaba a Ranar Kiyama. Kuma ya tabbata a cikinta yana wulakantacce. Sai wanda  ya tuba kuma ya aikata aiki na kwarai, to wadancan Allah Yana musanya miyagun ayyukansu da masu kyau. Allah Ya kasance Mai gafara mai jinkai. Kuma wanda ya tuba kuma ya aikata aiki mai kyau, to lallai ne sai ya tuba zuwa ga Allah. Kuma (Bayin Mai rahama su ne har wa yau) wadanda suke ba su yin shaidar zur kuma idan sun shude ga yasassar magana sai su shude suna masu mutunci. Kuma (su ne) wadanda suke cewa, “Ya Ubangijinmu! Ka ba mu sanyin idanu daga matanmu da zuriyarmu kuma Ka sanya mu shugabanni ga masu takawa. Wadannan ana saka musu da bene (a Aljanna), saboda hakurin da suka yi, kuma a hada su a cikinsa da gaisuwa da aminci. Suna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni. Ka ce: “Ubangijina ba Ya kula da ku in ba domin addu’arku ba. To lallai ne, kun karyata, saboda haka al’amarin ya zama malizimci.”

A cikin wadannan ayoyi masu girma na karshen Surar Furkan Allah Madaukaki Ya siffanta halayen bayinSa wadanda Ya daukaka su Ya jingina su gare Shi. Bayin Mai rahama su ne suka samu sharafi na jingina su zuwa ga Allah. Don haka idan ya kasance akwai masu bauta wa Shaidan da dawagitai da masu bauta wa sha’awoyinsu, to Mai rahama ba Ya maraba da su, domin su bayin Shaidan ne. (Duk wanda ya karkace daga hanyar kwarai shi Shaidan ne).

Ya bayin Allah! Wadannan su ne bayin Allah, jingina su zuwa ga Allah da sunanSa na Mai rahama nuni ne da cewa (Allah) Shi ne asalin rahama.

Ya bayin Allah! A yau muna da ’yan siyasa masu imani muminai, amma akasarinsu faksikai ne. Fasikai daga cikin ’yan siyasa su ne wadanda suke tattalin ashararai suke tattalin fitina da kisa da tayar da zaune-tsaye da jawo jidali da duk wani abu da zai hana ’yan kasa yin barci.

Ya bayin Allah! Su fasikai ne kuma ba su yi imani da Allah ba, sai dai sun yi imani da Shaidan da dagutu. “Idan aka ce su yi sujuda (kankan da kai) ga Mai rahama, sai su ce mene ne kuma Mai rahama? Shin za mu yi sujuda ne ga abin da kake umartarmu, sai su kara guduwa.” Idan ya kasance wadannan mutane sun jahilci wane ne Mai rahama, to akwai wadansu mutane da suka san Mai rahamar suke tsoronSa suke girmama Shi a kan hakkin girmama Shi. Suna ba Shi hakkokinSa. Don haka ku kasance daga cikin wadannan bayi na Mai rahama ko daga wace jam’iyya kuka fito. Kada ku yarda bambancin jam’iyya ya sa ku jawo abin da zai cutar da jama’ar kasa ko a zubar da jini ko a yi kashe-kashe ko a lalata dukiya.

Ya bayin Allah! Ga siffofi da dabi’unsu nan ga wanda yake son ya riske su.

Wani ya rera cewa:

“Kada ka ce mai rabo ya wuce,

Duk wanda ya bi hanyarsu zai riske su.”

Za mu daddale wadannan siffofi a huduba ta biyu. Lahula wala kuwwata illa billahl aliyyil azim.

Huduba ta Biyu:

Godiya ta tabbata ga Mai rahama Wanda Yake cewa: “Kada ka yi tafiya a kan kasa kana mai alfahari kana kumbura da nuna kasaita. Ka sani lallai ne kai ba za ka iya huda kasa ba saboda isa da karfi, kuma ba za ka kai tsawon duwatsu ba.” Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya a gare Shi. Kuma na shaida lallai Shugabanmu Annabi Muhammad BawanSa ne kuma ManzonSa ne wanda yake cewa: “Fitina tana barci kuma Allah Ya la’anci wanda ya tada ita.” Ya Ubangiji Ka kara tsira da aminci a gare shi da taslimi.

Ya bayin Allah! Kamar yadda muka fadi dazu daga cikin siffofin bayin Mai rahama ba bayin Shaidan akwai:

1.Tawali’u da hakuri, mutum ya yi tawali’u idan ya samu mulki ko wani iko. Kuma ya yi hakuri wajen tafiyar da harkokin jama’a. Sannan ya yi hakuri idan bai samu mulki ba

  1. Tsayuwar dare wajen ibada. Duk wanda yake neman wani abu a duniya to ya nema a wurin Allah musamman ta wajen yin nafilfili cikin dare yana ganawa da Ubangijinsa yana gaya masa bukatunsa. Kada ya kuskura ya je wurin boka ko mai duba ko ya aikata wani abu da matsafa za su nuna masa don ya samu mulki.
  2. Neman tsarin Allah daga wuta. Duk abin da mutum zai yi ya rika tunawa cewa ba fa duniya ce iyakar magana ba. Akwai Lahira kuma a Lahira gida biyu ne, Aljanna ko wuta. Don haka ya kauce ga duk abin da zai kai shi ga shiga wuta kuma ya nemi tsarin Allah daga shiga wutar.
  3. Tsaka-tsaki wajen ciyarwa. Kada mutum ya kuntata wa iyalansa ko wadanda suke karkashinsa wajen ciyarwa. Kuma kada ya yi almubazzaranci. Ya tsaya tsaka-tsaki kamar yadda aya ta gabata.
  4. Kadaita Allah. Bawa ya kadaita Allah wajen bauta da yarda da kaddararSa da ikonSa da buwayarSa da juya al’amuranSa.
  5. Gudun fitina. Kada wani ya tayar da fitina a kan wannan zabe da ke tafe. Ku lura akasarin ’yan siyasar da suke neman mukamai suna kwashe ’yan’yansu da iyalansu su kai kasashen waje saboda gudun kada fitina ta tashi ta shafe su. To me zai sa ku talakawa ku rika kashe-kashe da kone-kone a kan wadancan mutane?
  6. Tuba ta gaskiya. Bawan Mai rahama yakan yi kokari ya tuba daga aikata barna da zunubi tuba ta gaskiya. Don haka ba zai yarda ya jefa kansa ga abin da zai sa ya rasa Lahirarsa don duniyar wani ba.
  7. Barin shaidar zur da guje wa lagawu.Wajibi ne Musulmi ya kasance mai guje wa shaidar zur, wato goyon bayan karya don biyan bukatun son kai. Kuma a guji lagawu ko yasassar magana da za ta iya jawo tashin-tashina.
  8. Rungumar Littafin Allah wajen karatunsa da aiki da koyarwarsa.
  9. Yin addu’ar neman gyaruwar iyalai da zuriyya.
  10. Fatar shiga Aljanna.

Tawali’u – farko wadannan siffofi shi ne cewa su ‘suna tafiya a kan kasa da sauki’ wato bayin Mai rahama suna tafiya a natse ba takama ko nuna isa da griman kai da jiji-da-kai. Ya bayin Allah! Galibi tafiya takan nuna irin dabi’ar mai yin ta. Ta nuna fasalinsa da abin da yake da su na jiji da kai da dabi’u. Namiji yana da tsarin tafiyarsa haka mace, shi ma mai girman kai yana da nasa salon tafiyar. Muminai masu tawali’u ne a lokacin da suke tafiya masu kankan da kai ne hatta a tafiyarsu.

Ya bayin Allah! Wajibi ne a kan duk Musulmin da yake da’awar shi Bawan Mai rahama ne ya kasance mai hakuri a kan dukan komai. “Ku nemi taimakon Allah da hakuri da Sallah.”

Ya ku bayin Allah! Abin da muke bukatarsa a yau da muke daf da zabe, shi ne mu guje wa fitina da kashe-kashe da kone-kone. Kuma dukan Bayin Mai rahama suna gudun fitina da kashe-kashe. Allah Madaukaki Ya ce: “Duk wanda ya kashe wani mumini da niyya (haka kawai da gangan), to sakamakonsa Jahannama ce…”

Manzon Allah (SAW) ya ce: “Musulmi shi ne wanda Musulmi suka kubuta daga harshensa da hannunsa.”

Ya ku ’yan siyasa Musulmi! Ku guji kisa ko fitina ko yin abin da zai jawo kisa ko fitina.

“Lallai Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunta hakkinsa. Kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci (ko rarraba kan jama’a). Yana yi muku wa’azi tsammaninku kuna tunawa.”

A cikin wannan aya akwai umarni guda uku akwai kuma hani guda uku wadanda wajibi ne a kan kowane Musulmi ya kiyaye su a kowane lokaci.

Imam  Sharafudeen Abdussalam Aliagan shi ne Babban Limamin Masallaicn NASFAT na Kasa da ke Abuja, kuma za a iya samunsa ta tarho mai lamba: 080347108620