✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojan gona ya fashe da kuka a Ibadan

Wani mutum mai suna Abdullahi Musa ya fashe da kuka lokacin da ’yan sanda suka nuna shi ga ’yan jarida bisa zarginsa da yin sojan…

Wani mutum mai suna Abdullahi Musa ya fashe da kuka lokacin da ’yan sanda suka nuna shi ga ’yan jarida bisa zarginsa da yin sojan gona ga Hukumar Kwastam, inda ake zarginsa da karbar kudi daga hannun mutane.                                                                                                                                            Da yake yi wa manema labarai bayani, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo Mista Shina Olukolu ya ce jami’an yaki da fashi da makami na rundunar ne suka kama mutumin a motarsa kirar Marsandi a kan babbar hanyar Oyo zuwa Ogbomoso.

Bayan kama shi jami’an masu sintiri a hanyar sun binciki  motar inda suka gano katin shaidar aiki na Hukumar Kwastam mallakar  mutumin da hotonsa sanye da kayan sarki na Kwastam da takardun bogi na mallakar motar da yake tukawa.

Aminiya ta zanta da Abdullahi Musa wanda hawaye ke fita daga idanunsa inda ya ce, “Gaskiya na aikata abin da ya sa aka kama ni kuma na yi nadamar abin da na aikata.”

Da yake amsa wata tambaya Abdullahi Musa cewa ya yi, “Ni mutumin Jihar Neja ce, amma ina zaune ne a Legas inda nake  kasuwancin kayan abinci. Ina hanyar zuwa gida domin yin bikin Sallah tare da iyalina ne aka kama ni.   Wannan shi ne karo na farko da na aikata irin wannan. Motar da nake tukawa mallakar dan uwana ne, wanda jami’in tsaro ne kuma bai da masaniyar na dauki motar tasa. Ina amfani da wadannan abubuwa na jami’an Kwastam ne domin samun damar tsallake shingen ’yan sanda a kan hanya.”

Kwamishinan ’Yan sandan ya ce, da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da Abdullahi Musa a gaban kotu domin yanke masa hukunci.