✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun dakile harin Boko Haram a sansaninsu na Borno

Wata majiya mai tushe daga hukumomin tsaro da kuma ‘yan sa kai sun nuna cewa, ana tsammanin rayuka sun salwanta bayan da wasu da ake…

Wata majiya mai tushe daga hukumomin tsaro da kuma ‘yan sa kai sun nuna cewa, ana tsammanin rayuka sun salwanta bayan da wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka yi yunkurin kai hari akan sansanin sojin Najeriya da ke jihar Borno a safiyar ranar Laraba.

Aminiya ta gano cewa, ‘yan tada kayar bayan sun biyo yankin Gwoza domin kai wa Sojojin sansanin yaki na 25 da ke garin Damboa hari a safiyar ranar Laraba, inda suka yi ruwan wuta akan sansanin.

Wani dan kungiyar sa kai a garin ya shaidawa Aminiya cewa, maharan sun je garin da motocin yaki guda biyu inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.

Ya kara da cewa, “Harin ya haddasa rudani a garin na Damboa, lokacin da wasu mahara na kungiyar Boko Haram suka kai wa sansani na 25 da ke garin hari. An yi bata kashi na tsawon awa biyu. A yanzu dai abubuwa sun lafa, amma akwai wadanda harin ya rutsa dasu. Mazauna garin sun tsere da rayukansu zuwa garin Chibok lokacin da aka kawo harin.”

Wata majiya daga hukumar tsaro ta tabbatar da faruwa lamarin, inda ta bayyana cewa rayuka da yawa sun salwanta daga bangarorin soja da na maharan.

Majiyar ta kara da cewa, “Nasan da faruwan harin wanda aka kaishi tun karfe 6:00 na safe, amma sojoji suna kokarin dakile harin. An samu salwanta rayuka a bangarorin biyu, amma sojojin suna samun nasara.”

Wakilinmu ya kuma gano cewa, maharan sun kai wani harin a kauyen Bwalakila mai nisan kilomita 4 daga garin Chibok a daren Laraba, amma babu wanda ya rasa ransa a harin.

Har yanzu dai babu wani bayani da sojoji akan lamarin.