✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun hallaka ‘yan Boko Haram 39 a Borno

Dakarun hadaka na sojin kasashen yankin Tafkin Chadi (MNJTF) sun samu nasaras hallaka ’ya’yan kungiyar Boko Haram 39 inda suka kwato makamai masu yawa daga…

Dakarun hadaka na sojin kasashen yankin Tafkin Chadi (MNJTF) sun samu nasaras hallaka ’ya’yan kungiyar Boko Haram 39 inda suka kwato makamai masu yawa daga hannunsu a wata fafatawa da suka yi a Kuros Kaura da ke Jihar Borno.

Wata sanarwa da ta fito daga Kakakin Dakarun Hadakar Kanar Timothy Antiigah ce ta tabbatar da haka, inda dakarun hadakar kasashen da ke yaki da mayakan Kungiyar Boko Haram a yankin Tafkin Chadi, sun ce reshe ne ya juye da mujiya a wannan dauki ba dadi, lokacin da ’yan ta’addan Boko Haram suka kai musu hari a yankin.

Sanarwar ta ce sojojin hadakar wadanda suke zaune cikin shiri sun mayar da martani ga maharan tare da karya lagonsu, kuma suka yi musu mummmunar illa.

Sanarwar ta kara da cewa, a yayin wannan gumurzu da suka yi a ranar Talatar da ta gabata, a ci gaba da aikin da suke yi a yankin da aka yi wa lakabi da ’Yancin Tafki, sun yi nasarar, hallaka mayakan Boko Haram 39 tare da kwace makamai masu dimbin yawa.

Sai dai sanarwar ta cean raunata dakarunta 20 a yayin ba ta kashin, wadanda aka kwashe su a jirgin saman soji aka fice da su daga yankin domin a je a yi musu magani, kuma suna samun kula.

Wata sanarwa kuma da ta fito daga Mataimakin Kakakin Sashi na 3 na Dakarun Operation Lafiya Dole

Kanar Ezindu Idimah ta bayyana cewa makaman da sojojin suka kwato daga ’yan ta’addan Boko Haram din bayan fafatawar sun hada da motocin da suke dauke da manyan bindigogin yaki guda biyu (2 d Gun Trucks) da bindigogin harbo jiragen sama guda biyu (2 d Anti Aircraft Guns) da bindiga kirar AK47 guda tara da bindiga kirar HK21 guda daya da bindigar harba roka guda hudu (4 d Rocket Propelled Guns).

Sanarwar ta ce sakamakon samun wannan nasara Shugaban Sojojin Kasar Chadi Janar Tahir Erda ya ziyarci Dakarun Operation ‘Yancin Tafki domin ya kara musu kaimi a kan yakin da suke yi. A jawabinsa lokacin ziyarar, ya yi kira ga dakarun cewa su kara ba da hadin kai a tsakaninsu, sannan ya ziyarci asibitin sojoji inda ya duba sojojin da suka samu raunuka a fafatawar.