✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe `yan bindiga 25 a Zamfara

Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta ce dakarunta  na ‘Operation Diran Mikiya’ sun tarwatsa sansanin ‘yan bindigar na unguwar Ajia yayin da suka kashe akalla…

Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta ce dakarunta  na ‘Operation Diran Mikiya’ sun tarwatsa sansanin ‘yan bindigar na unguwar Ajia yayin da suka kashe akalla 25 a  Ajia da Wonaka a karamar hukumar Birnin Magaji da ke jihar Zamfara.

Kakakin rundunar sojojin saman Iya Kwamando Ibikunle Daramola, ya ce dakarunsu sun fara kaiwa ‘yan bindigar farmaki ne a ranar 4 ga Afrilu 2019 ta hanyar bin matakan sirri, sojojin sun bankado cewa, maharan na amfani da wasu wurare a unguwar Ajia a matsayin maboya makaman su.