✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kubutar da mutum 8 da aka yi garkuwa a Kaduna

Rundunar sojoji ta ‘Operation Whirl Punch’ da ke Kaduna sun kubutar da mutum da takwas da aka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna zuwa…

Rundunar sojoji ta ‘Operation Whirl Punch’ da ke Kaduna sun kubutar da mutum da takwas da aka yi garkuwa da su a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari ranar Laraba.

Sojojin sun yi nasarar kubutar da wadanda aka kama ne a wanin samame da suka kai a maboyar su da ke kauyen Labi a karamar Hukumar Chikun jihar Kaduna, an dai kubutar da su ne da misalign karfe 5 na yamma ranar Laraba, bayan yin garkuwan da su.

Mutanen da aka kama matafiya ne da suke hanyar su daga Kano zuwa Ilorin, sai ‘yan bindigar suka tare su suka shiga daji da su. Kamar yadda jami’an sojojin suka bayyanawa majiyar Kamfanin Dillancin Labarai NAN.