✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun tarwatsa sansanin Boko Haram a  Sambisa

Rundunar sojojin saman Najeriya karkashin dakarun Operation Lafiya Dole, sun sanar da cewa sun gano moboyar ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa da ke jihar…

Rundunar sojojin saman Najeriya karkashin dakarun Operation Lafiya Dole, sun sanar da cewa sun gano moboyar ‘yan Boko Haram a dajin Sambisa da ke jihar Borno. Inda suke gudanar da taron tattaunawa.

Kakakin rundunar sojojin Najeriya Air Commodore Ibikunle Daramola, ya ce dakarun sun samu nasarar tarwatsa sansanin mayakan ne ta hanyar samun bayanan sirri a ranar 13 ga watan Oktoba 2019.

Ibikunle, ya kara da cewa sansanin mayakan ya kasance wajen da Kwamandojin kungiyar ke zuwa don bayar da umarnin kai hari ga fararen hula.