✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Suleiman ya zama shugaban Majalisar Bauchi

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Ningi ta tsakiya a Majalisar dokokin jihar Bauchi Alhaji Abubakar Y. Suleiman, ya zama shugaban Majalisar dokokin jihar. An zabi…

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Ningi ta tsakiya a Majalisar dokokin jihar Bauchi Alhaji Abubakar Y. Suleiman, ya zama shugaban Majalisar dokokin jihar.

An zabi sabon shugaban Majalisar dan jam’iyyar APC ne a yau Alhamis a zauran majalisar inda mafi yawan wadanda suka zabi shugaban, masu goyon bayan sabon Gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed.

Mataimakin Shugaban Majalisar jihar Bauchi Ahmed Kawule

Yayin da suka zabi Danlami Ahmed Kawule na Jamiyyar PDP daga Mazabar Zungur Galambi a matsayin Mataimakin Shugaban Majalisa.

Dan majalisa mai wakiltar Hardawa, Babayo Muhammad ne ya fara zabar sabon shugaban majalisar a zauren.