✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sulhu da ’yan bindiga ya zame alheri ga Katsina  – Wurma

Kwamared Kabiru Amiru Wurma shi ne Sakataren Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa reshen Jihar Kebbi, dan asalin Jihar Katsina ya yaba kan yadda sasantawa da…

Kwamared Kabiru Amiru Wurma shi ne Sakataren Kungiyar ’Yan jarida ta Kasa reshen Jihar Kebbi, dan asalin Jihar Katsina ya yaba kan yadda sasantawa da masu garkuwa da mutane da ’yan bindiga a  Jihar Katsina ta yi tasiri:

 

Kai dan asalin Jihar Katsina ne kuma a yankin da matsalar tsaro ta yi kamari yaya yanayin tsaro yake yanzu bayan sasantawa da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane?

A watannin baya Jihar Katsina ta sha fama da ukubar masu garkuwa da mutane da masu satar shanu. Akwai lokacin da muke jin cewa masu garkuwa da mutane da sace shanunsu sun mamaye yankunan jihar Kudu da Tsakiya da Arewacin Jihar Katsina.

Kuma wani lokaci sai dai ka ji cewa sun tare hanyoyi da ke zuwa wasu kananan hukumomin jihar an sace mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Wannan matsala ta ci gaba da faruwa har zuwa farkon bana, lokacin da aka samu canjin gwamnatin a Jihar Zamfara inda Gwamna Bello Matawalle ya fito da shirin sasantawa da sulhu da ’yan ta’adda masu garkuwa da mutane a jiharsa, domin a lokacin da ya fara wannan tsarin kamar wasa, amma a karshe shirin ya yi matukar tasiri.

A ranar wata Litinin, masu garkuwa da mutane sun yi dirar mikiya a garinmu na Wurma inda suka zagaye garin da misalin karfe 11:30 na dare wannan shi ne farmaki mafi muni a Jihar Katsina domin a wannan ranar ’yan ta’adda 300 ne suka yi wa garin na Wurma kawanya suka sace ’yan mata 48 da tsohon Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Kurfi, baya ga shanu  da raguna fiye da 100 inda suka tafi da su zuwa Dajin Rugu har sai da aka biya kudin fansa kimanin Naira miliyan 10 sannan suka sako su.

Hakan ya sa Gwamna Aminu Bello Masari ya kasa tsaye ya kasa zaune, har ya ce “Ba zan bari wannan matsalar tsaro da garkuwa da mutane da satar shanu a jihar nan ta ci gaba ba. Domin idan na mutu me zan gaya wa Allah a kan mulkin mutanen Katsina?”

Bisa ga hakan ya dauki mataki irin na abokin aikisa Gwamnan Zamfara don hada taron sasantawa da sulhu da shugabannin ’yan ta’addan masu garkuwa da mutane a jihar. Kuma ya kai ziyara ga shugabannin masu garkuwa da mutanen, na farko a yankin Kankara sai na biyu a yankin Safana kuma ya kai Batsari da Jibiya don tattaunawa da shugabannin masu ta’asar don a samu maslaha.

Kana ganin an samu zaman lafiya a Jihar Katsina yanzu?

An samu zaman lafiya a Jihar Katsina. Yanzu akwai kwanciyar hankali da zaman lafiya. Saboda hakan wannan abin yabawa ne, ya zama dole mu yaba wa tsarin da Gwamna Aminu Masari ya fito da shi na yin sulhu da wadannan ’yan bindiga.

Tunda tsaro ya dalilin sasantawa da Gwamna Masari ya yi da ’yan bindigar ko akwai wani kira da za ka yi?

Kirana zuwa ga ’yan bindigar da suka mika makamansu ga gwamnatin Jihar Katsina cewa don Allah su tabbatar da sun rike alkawarin dokokin da aka shimfida yayin gudanar da sulhun da aka yi tsakaninsu da gwamnati.

Haka kuma don Allah su daina satar mutane suna garkuwa da su a kauye ko a garuruwan mutane, ko kan hanya.Har ila yau ina kira ga jami’an tsaro da kada su karya alkawalin da aka yi da wadannan mutane su bar mutanensu su yawata a cikin al’umma kamar yadda suka nema na zuwa kasuwa ko masallaci kamar yadda kowane mutum ke iya tafiya.