✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta kashe dan kishiyarta ta jefa a rijiya

Ana zargin wata mai suna Grace Jacob Maisamari da laifin kashe dan kishiyarta dan shekara hudu mai suna Ritse Micah tare da jefa shi a…

Ana zargin wata mai suna Grace Jacob Maisamari da laifin kashe dan kishiyarta dan shekara hudu mai suna Ritse Micah tare da jefa shi a rijiya.

Ana zargin an daure hannuwa da kafafuwan yaron da ke zaune da mahaifansa a Karamar Hukumar Akwanga kafin a kashe shi, inda aka iske gawarsa a wata  rijiya a Unguwar Eggon da ke yankin Garaku a Karamar Hukumar Kokona a Jihar Nasarawa.

An tsinci gawar tasa ce bayan kwana daya da sace shi a cikin rijiyar a Karamar Hukumar Kokona da ke nesa da Karamar Hukumar Akwanga, lokacin da wadansu mata suka je rijiyar don dibar ruwa.

Mahaifin yaron mai suna Micah Kapechi ya ce, “An sace yaron ne bayan an shigo gidana da tsakar dare ina cikin barci mai nauyi. An bar mini wasika cewa, in biya Naira miliyan hamsin a matsayin kudin fansa, sannan kada in gaya ’yan sanda, domin sun san da wannan harka. Sannan sun gargade ni cewa idan na shaida musu, za su kashe ni.”

Mahifin yaron wanda ma’aikacin Karamar Hukumar Kokona ne, ya kara da cewa kwana daya bayan an sace yaron, da aka gan shi, sai ’yan sanda suka ciro shi, sannan aka baza a kafar sadarwa ta facebook.

Bugu da kari, mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Nasarawa, ASP Sama’ila Usman ya ce sun tsananta bincike, inda ya kai su ga kama wacce ake zargi, wato Grace Jacob Maisamari, wacce kuma take auren mahaifin yaron. Ya ce rundunarsu na ci gaba da bincike kan al’amarin domin gurfanar da wadanda ake tuhuma gaban kotu.