Da Dumi Dumi

Ta kashe kanta akan mutuwar auren mahaifanta

Wata yarinya `yar kimanin shekara 17 mai suna Sadiya Shehu a unguwar Tudun Murtala a yankin Karamar Hukumar Nassarawa cikin Jihar Kano, ta kashe kanta saboda rashin fahimta da ta shiga tsakanin mahaifiyarta da mahaifinta wanda ya yi sanadiyar rabuwarsu.

Yarinyar ta rasu ne bayan da ta kwankwadi madarar fiya-fiya  wanda ke ajiye a dakin mahaifiyarta don kashe sauro da sauran kwari.

A lokacin da Aminiya ta ziyarci gidan su yarinyar a unguwar Tudun Murtala ta iske gungun mutane suna ta shiga gidan don jajantawa iyalan marigayiyar.

Malam Shehu Lawan shi ne mahaifin marigayiya Sadiya ya bayyana cewa, marigayiyar ta kashe kanta ne akan dan ‘kankanuwar matsala’ da ta auku tsakaninsa da mahaifiyarta wanda kuma daga baya suka warware matsalar.

“Ina da matsala da mahaifiyarta wanda hakan ya jawo ba ta yi farin ciki da lamarin ba domin ta yi ta kuka akan hakan daga baya na gaya mata cewa abin ya wuce. Da sassafe na tashi na fita na bar Sadiya da sauran `yan uwanta lafiya. Ni dai ina wurin aikina sai aka yi min waya cewa, na garzaya da ita asibiti. Likitoci sun yi iyakar kokarinsu amma da yake Allah Ya kaddara haka sai ga shi ta riga mu gidan gaskiya”.

ADVERTISEMENT

Da Aminiya ta tambaye shi ko an yi wa Sadiya miji, mahaiin nata ya bayyana cewa tana da manemi? “Domin wani lokaci na karshe da na yi magana da shi ya yi alkawarin zai turo magabatansa a da zarar mahaifinsa ya dawo daga Saudiyya za su zo a yanke maganar aure. Sai dai da yake kaddara ta riga fata auren ba zai yi wu ba saboda amaryar ta tafi.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya