Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Ta kashe saurayinta ta dafa namansa ta raba wa makwabta

Ana tuhumar wata mata ’yar kasar Moroko da  laifin kashe saurayinta tare da dafa namansa ga makwabta ma’aikata ’yan kasar Pakistan da suke Daular Larabawa (UAE), kamar yadda matar ta bayyana lokacin da ake tuhumarta.

Matar ta kashe saurayin ne wata uku da suka gabata, amma kwanan nan aka gano laifin lokacin da aka ga hakorin marigayin a cikin injin markade ‘blender’.

ADVERTISEMENT

Jaridar The National ta kasar ta ce, matar ta bayyana wa ’yan sanda abin da ya faru a tsakaninta da saurayinta a matsayin tsatsauyi ne mai kamar hauka ya sa ta aikata laifin, kamar yadda sashin Ingilishi na BBC ya ruwaito.

Matar wanda za ta shiga shekara ta 30 za a ci gaba da tsare ta har zuwa lokacin da za a kammala bincike.

ADVERTISEMENT

Matar ta ce, tana hulda da saurayin nata kusan shekara bakwai da suka gabata, kamar yadda majiyar The National ta sanar, matar ta ce, ta kashe saurayinta ne lokacin da ya bayyana mata cewa yana shirin auren wata mata daban daga kasar Moroko.

Sai dai ’yan sandan ba su bayyana yadda matar ta kashe saurayin ba, amma sun ce budurwar ta girka naman  saurayin da shinkafar gargajiya ga wasu ma’aikata’ yan kasar Pakistan da suke aiki a makwabtanta.

An dai gano mutuwar saurayin ne lokacin da dan uwansa ya fita nemansa a birnin Al Ain, wanda ke gabar garin Oman. A nan aka fara gano hakoran mutum a cikin bilanda, kamar yadda aka wallafa a jaridar.

Mutumin ya kai karar bacewar dan uwansa ne ga ’yan sanda, inda suka yi wa hakoran gwajin DNA don tabbatar da hakoran na wanda aka kashe ne.

A cewar ’yan sanda da farko matar ta fada wa dan uwan wanda ya rasun, cewa saurayinta ya fita daga gida.

Kafar labarai ta Dubai Gulf News ta ce, matar ta ce saurayin ya fadi ne lokacin da ’yan sandan ke bincike. Ta bayyana cewa, ta gayyaci makwabtanta su taimaka mata, bayan ta kashe saurayin.

Daga bisani matar da ta aikata kisan an kaita asibiti don bincikar kwakwalwarta.