Search
Subscribe
Ta tabbata Saif al-Islam Gaddafi zai yi takarar Shugaban Kasa a Libya

Ta tabbata Saif al-Islam Gaddafi zai yi takarar Shugaban Kasa a Libya

Dan tsohon Shugaban Kasar Libya, marigayi Kanal Muammar Gaddafi mai suna Saif al-Islam zai tsaya takarar Shugaban Kasa a zaben da za a yi a watan Disamba na bana.

Jaridar The Telegraph ce ta ruwaito hakan daga rahotannin da ta samu daga kafafen yada labarai na kasar Libya.

Shi dai Saif al-Islam Gaddafi, wanda tun a zamanin mulkin mahaifinsa ake sa ran shi ne zai gaje shi, ya kasance cikin wadanda Kotun Duniya wato ICC ke nema ruwa a jallo bisa zarginsa da hannu a kashe-kashen da ya wakana a kasar a shekarar 2011 a lokacin da suke kokarin murkushe masu tada kayar baya a kan mulkin Gaddafi.

Jam’iyyar Front Party ta kasar ce ta sanar da batun cewa Saif al-Islam zai tsaya takara a zaben mai zuwa, kamar yadda rahoton ya nuna.

Wani mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum a kasar, Khaled Guel ya shaidawa jaridar al-Araby al-Jadeed cewa ya kamata kasar Libya ta kawo karshen rabe-raben kai a tsakanin ‘yan kasar.

“Mutane suna kara shiga cikin matsanancin hali, kuma babu tabbas a kan abin da zai faru nan gaba. Don haka ne ma wasu mutane suke ganin hanya daya da za a iya ceto kasar nan ita ce zaben Saif al-Islam,” inji shi.

Shi dai Saif al-Islam yana cikin wadanda aka tsare bayan an kifar da gwamnatin mahaifinsa, inda ya shafe kusan shekara 6.

A shekarar 2015 kuma wata kotu a birnin Tripoli ta yanke masa hukuncin kisa. Amma kuma sai kwatsam aka sake shi bara, bayan ya samu yafiya.

Har yanzu bai bayyana kansa ba, kuma har yanzu babu labarin asalin inda yake, amma Jam’iyyar Front Party ta ce kwanan nan zai fito fili ya gana da manema labarai na kasar.

Saif al-Islam yanzu yana da shekara 45 ne a rayuwa kuma shi ne dan Gaddafi na biyu, kuma yana cikin wadanda suka bayar da gudunmuwa a zamanin mulkin mahaifinsa Gaddafi.

Ana zarginsa ne da kalamun ingiza rikici da kashe masu zanga-zanga.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin