Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Ta’aziyar Sa’adatu Muhammad Fawu

Ta’aziyar Sa’adatu Muhammad Fawu

Allah ya yi wa Hajiya Sa’adatu Muhammad Fawu, Wakiliyar Muryar Amurka wacce ake wa lakani da Gwagwo Sa’a Rasuwa a cikin dare ranar Talatar da ta gaba 2 ga watan Disamba bayan ta yi fama da doguwar rashin lafiya.

Gwaggo Sa’a, kafin rauswarta ita ce wakiliyar sashin Hausa na gidan radiyon muryar Amurka a bangaren lafiya a jihar Kano kafin daga baya a maida ita yankin Arewa maso gabas, da suka hada da jihohin Borno da Yobe da kuma Gombe.
Hajiya Sa’adu Fawu, kafin ta fara aiki da gidan Radiyon muryar Amurka Malamar Turanci ce da hukumar samar da ilimi na bai daya (State Unibersal Basic Education board), ta dauke ta aikin koyarwa a Firamare ta Model da ke fadar jihar Gombe a shekarar 2000, da ta bar
aikin koyarwa ta kama aiki da kafar Talabijin Mallakar jihar Gombe (GMTb) har zuwa shekarar 2006, inda ta samu aiki da gidan radiyon muryar murka (bOA) Sashin Hausa a matsayin wakiliya a bangaren kiwon lafiya a ofishinsu da ke Kano.
A shekarar 2009 ne saboda wata bukata da ta taso na neman wakili a shiyar Arewa maso gabas, sai aka dawo da ita garin Maiduguri inda ta zama mai aika rahotanni da suka shafi shiyar Arewa maso gabas, wanda ita take zaga dukkan jihohin Arewa maso gabas din guda shida.
Hajiya Sa’adatu Fawu an haife ta ne a garin bare na karamar hukumar billiri a jihar Gombe a ranar 1 ga watan Afirilu na shekarar 1972 kimanin shekara 42 da suka wuce, kuma ita ce ‘yar auta a wajen mahaifinta Alhaji Muhammad Fawu Galadiman Tangale, wanda ya haife ta a lokacin yana da shekaru 75 a duniya.
Ita dai Sa’adatu Fawu mace ce wacce ba ta da girman kai, kuma take hababa da mutane, domin ko yaya kake ba ta kyamarka, wai don ganin tana aiki a kafar yada labarai ta Amurka, har shawarwari take bai wa sauran tsofaffin abokan aikinta da suka yi aiki tare a gidan Talabijin na jihar Gombe ta hanyar da za su inganta aikinsu su zama suna iya aiki da na’urar zamani wajen dauko rahotanni (Digitalization).
Gwagwo Sa’a, ta yi katatun Firamare ta Central da ke garin billiri, bayan ta gama sai ta tafi Sakandaren ‘yan mata ta Women Teachers Collage WTC ta Kaltungo inda ta kammala a shekarar 1992, bayan ta gama Makarantar Sakandare a shekarar 1995 sai iyayenta suka yi mata aure, tana da auren ne ta tafi kwalejin ilimi na gwamnatin Tarayya ta Gombe (FCE) a shekarar 1996 ta gama a shekara ta 2000 ta samu takardar shaidar karatu ta NCE a bangaren Turanci, daga nan sai ta sake tafiya kwalejin koyon sana’o’i ta gwamnatin tarayya da ke garin Bauchi (Federal Polytechnic), inda nan kuma ta samu takardar shaidar karatu ta (Adbance certificate) a bangaren aikin jarida a shekara ta 2008.
A tsakanin shekara ta 2009 zuwa 2011 ne ta tafi jami’ar Maiduguri ta samu takardar shaidar Digiri din ta na farko a bangaren turanci English Education. Kasancewar ta wakiliyar lafiya na bOA Sa’adatu Fawu ta halarci Kwasa-kwasai Masu yawa a cikin gida da kuma wajen wadanda hukumomin kasashen turai irin su UNDP da UNICEF da USAID suke shiryawa da kuma irin wanda sashin Hausa na Muryar Amurka suke shirya musu a matsayin wakilansu.
Ita dai kafin ta rasu mamba ce a kungiyar mata ‘yan jarida ta kasa Nigerian Association of Women Journalist (NAWOJ) kuma mamba a kungiyar Nigerian Union of Journalist (NUJ) kuma ita ce Sakatariyar kudi ta NUJ
na jihar Borno.
Shugaban kungiyar Yan jaridu ta kasa reshen jihar Gombe Alhaji Alhassan Yahya Abdullahi, tuni ya jajantawa kungiya Mata yan jaridu ta kasa da kuma kungiyar yan Jaridun bisa rasuwar Gwagwo Sa’a. Alhassan Yahya, yace rasuwar Gwagwo babban rashi ne ba ga iyalanta kadai ba jiha ne dama kasa baki daya akayi rashin daga nan sai ya yi addu’ar Allah ya jikanta.
Hajiya Sa’adatu Fawu ta rasu ne a wani asibiti a babban birnin tarayyar Abuja kuma tuni akayi jana’izar ta kamar yadda addinin musulunci ya tanadar ta rasu ta bar maigidanta da Yarta daya Aisha mai kimanin shekaru goma sha takwas da haihuwa wacce yanzu haka take karatu a kasar Turkiya Allah ya jikanta da rahama amin.