✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ta’aziyya:  Sanata Babayo Gamawa ya bar gibi mai wuyar cikewa

A ranar Juma’ar da ta gabata ce al’ummar Jihar Bauchi suka yi babban rashi na tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Sanata Babayo Garba Gamawa. Dubban jama’a…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce al’ummar Jihar Bauchi suka yi babban rashi na tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Sanata Babayo Garba Gamawa. Dubban jama’a daga ciki da wajen jihar suna ta mika sakon ta’aziyarsu a kan wannan babban rashi da ya bar gibi mai wuyar cikewa.

A sakonsa na ta’aziyya, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Babayo Gamawa a matsayin mutum mai tarin basira, kuma ma’aikaci na gaske, haziki mai kokari. Wata sanarwa daKakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce hakika rashin Babayo Gamawa ba karamin rashi ba ne. Ta ce marigayin ya ba da gudunmawa ga ci gaban dimokuradiyya a kasar nan, kuma dan siyasa da ba ya gudun jama’arsa. Sai ya yi addu’ar Allah Ya jikansa da gafara, kuma Ya bai wa iyalansa da al’ummar Jihar Bauchi da Najeriya hakurin jure wannan rashi.

Shi kuwa Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad bayan ya halarci jana’izar mamacin ya yi addu’ar Allah Ya jikansa Ya gafarta masa, inda ya bayyana Sanata Babayo Gamawa a matsayin mutumin kwarai wanda ya yi aiki tukuru domin ci gaban jihar.

A zantawar Aminiya da mutane daban-daban a garin Gamawa sun bayyana marigayin da cewa mutum ne mai taimakon makwabta. Wani daga cikinsu ya ce “Idan marigayin zai aurar da ’ya’yansa yakan tambaya a makwabtansa ko akwai yaran da suka isa aure sai ya hada ya yi musu kayan daki irin wanda ya yi wa ’ya’yansa ya aurar da su baki daya, gaskiya samun irinsa sai an tona Allah Ya yafe masa.”

Wani aminin marigayin, Alhaji Garba Gadau ya ce, “Mun tashi tare da Babayo mun zama ’yan uwa tamkar uwa daya uba daya, mutum ne mai zumunci, ga son alheri, wanda ba ya gudun jama’a. A kullum ba abin da yake so kamar ya zauna lafiya da mutane ya kuma taimake su. Hakika mun yi rashi, da wuya ka ga mutum irinsa wanda ba ya kyamar kowa, kullum da mu abokansa da mutanen karkararsu tare  muke cin abinci kwarya daya.”

An haifi marigayi Sanata Babayo Gamawa a ranar 2 ga Fabrairun 1966. Ya yi karatu a Jami’ar Jos inda ya samu takardar babbar shaida kan saye da samar da kayayyaki, (Purchasing and Supply), an zabe shi  dan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi da ke wakiltar Gamawa a shekarar 2007 kuma ya zama Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, daga bi sani aka nada shi Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi a lokacin Gwamna Isa Yuguda, bayan tsige tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar marigayi Alhaji Gaba Muhammad Gadi. Da aka kammala zangon farko na mulkin a shekarar 2011, sai ya tsaya takarar Sanata maimakon tsayawa takara da Gwamna Isa Yuguda a karo na biyu. Ya samu nasarar zama Sanata mai wakiltar Bauchi ta Arewa kuma ya rike mukamai da dama a Majalisar Dattawan.

Sanata Babayo Gamawa ya nemi tsayawa takarar Gwamnan Jihar Bauchi a shekarar 2015 a karkashin Jam’iyyar PDP bai samu nasara ba, inda aka tsayar da Alhaji Auwalu Jatau. Kuma an zabe shi Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa daga baya.

Kafin fara yakin neman zaben  bana, Sanata Gamawa ya samu matsala da Jam’iyyar PDP inda aka zarge shi cewa ba ya halartar tarurrukan jam’iyyar, da aka yi yunkurin dakatar da shi, sai Jam’iyyar APC ta fara zawarcinsa, kuma bayan ganawarsa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari sai ya koma Jam’iyyar APC, kuma aka ba shi mukamin Darakta Janar na yakin neman zaben Gwamna Muhammadu Abdullahi Abubakar na Jihar Bauchi, zaben da Jam’iyyar PDP ta samu nasara.

Ya rasu ya bar matan aure hudu da ’ya’ya 16 da kuma mahaifiyarsa.   An yi jana’izarsa a garin Gamawa mahaifarsa bisa tsarin addinin Musulunci, inda dubban jama’a suka halarta.

Allah Ya jikansa Ya gafarta masa.