✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Takaitaccen tarihin marigayi Hassan Sarkin Dogarai

Marigayi Alhaji Hassan Adamu, wanda aka fi sani da Hassan Sarkin Dogarai, shi ne Sarkin Dogarai na uku da marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero…

Marigayi Alhaji Hassan Adamu, wanda aka fi sani da Hassan Sarkin Dogarai, shi ne Sarkin Dogarai na uku da marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya nada a mastayin Shugaban Dogarawan Sarki a 1990. Kafin nadin marigayi Hassan a matsayin Sarkin Dogaran Kano, marigayi Ado ya nada wadansu mutum biyu a baya, wato marigayi Sarkin Dogarai Dan Wudil da marigayi Sarkin Dogarai Adamu. Kuma bayan rasuwar Sarkin Dogarai Adamu ne aka nada Alhaji Hassan Sarkin Dogarai, sannan bayan rasuwarsa aka nada Sarkin Dogarai na yanzu, Alhaji Danbala.

Sai dai sabanin Sarkin Dogarai Adamu da Sarkin Dogara Dan Wudil, Hassan ba Bafade ba ne. Asalinsa direba ne da ke sana’ar tuka mota kafin daga baya ya zama hadimi ga Galadiman Kano, marigayi Alhaji Tijjani Hashim. Galdiman Kano Tijjani Hashim shi ne wanda ya fara nada shi a matsayin Shamakinsa kuma ya zama silar shigarsa cikin fadar Kano.

A 1990 ne, bayan rasuwar Sarkin Dogarai Dan Wudil, marigayi Turakin Kano kuma daga baya Galadiman Kano Tijjaji Hashim ya roki Sarkin Kano Ado Bayero alfarmar ya nada Hassan a matsayin Sarkin Dogarai saboda tsananin biyayyarsa da jarumtakarsa, sannan ga soyayyar da yake nunawa ga Sarkin.

Marigayi Sarkin Dogarai Hassan yana zaune ne tare da iyalinsa a Unguwar Sagagi da kebirnin Kano, kusa da gidan mahaifiyar marigayi Sarki Ado Bayero, kafin daga bisani ya koma gidan Sarkin Dogarai da ke Unguwar Dogarai daf da gidan Sarkin Kano.

Sarkin Dogarai Hassan ya shahara a cikin sarakunan Dogaran Kano saboda karfi da jarumta da tsananin biyayyarsa ga Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero.

Alhaji Hassan Sarkin Dogara sharcecen mutum ne, saboda girma da tsayinsa har kirari ake yi masa da Bishiya.

Wani dan asalin Unguwar Dogarai, mai suna Ibrahim Mu’azzam Sadauki da ya san marigayi Hassan Sarkin Dogarai, ya ce “Marigayi Hassan ya fara haduwa ne da shahararren mawakin Hausar nan, Alhaji Mamman Shata, yayin da yake sana’arsa ta tuka mota. Bayan Hassan ya zama Sarkin Dogarai ne, sai Alhaji Mamman Shata ya rera masa wakar “Hassan Sarkin Dogarai,” wakar da ta kara fito da sunansa a duniya.”

Yanzu haka iyalan marigayi Sarkin Dogarai Hassan sun koma gidansa da ke Unguwar Sagagi inda suke ci gaba da rayuwa bayan rasuwar mahaifinsu.

Allah Ya jikansa da rahama, amin, Mun samo wannan rubutu ne daga shafin Hausawa