✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Taliban ta kai hari kan sojojin Afghanistan

Kungiyar Taliban da ke Afghanistan ta kaddamar da hari kan sansanin sojin gwamnati, sa’o’i bayan kawo karshen tsagaita wuta da ta yi, matakin da ake…

Kungiyar Taliban da ke Afghanistan ta kaddamar da hari kan sansanin sojin gwamnati, sa’o’i bayan kawo karshen tsagaita wuta da ta yi, matakin da ake ganin zai rusa yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kulla da kasar Amurka a karshen mako.

Wani jami’in Ma’aikatar Tsaron Kasar ya ce, Taliban ta kai hare-hare a kan sojojin gwamnati a yankuna 13 daga cikin 34 da ake da su, wadanda suka hallaka soji biyu.

A ranar 10 ga watan nan ake sa ran kungiyar za ta fara tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin Afghanistan bayan yarjejeniyar da ta kulla da Amurka a makon jiya.

Yarjejeniyar ta kunshi ganin Taliban ta saki fursunonin yaki 1,000 da take tsare da su, yayin da gwamnati za ta saki mayakan kungiyar kusan 5,000, abin da Shugaban Kasar Ashraf Ghani ya ce ba zai amince da shi ba.