✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tambuwal ya koka da fadar shugaban kasa

Ganin yadda Gwamnatin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin Gwamna AbdulAziz Yari Abubakar take gudanar da ayyukan hanyoyin da ke cikin jihar, musamman ma hanyoyin gwamnatin tarayya…

Ganin yadda Gwamnatin Jihar Zamfara, karkashin jagorancin Gwamna AbdulAziz Yari Abubakar take gudanar da ayyukan hanyoyin da ke cikin jihar, musamman ma hanyoyin gwamnatin tarayya dake cikin jihar, shuagaban Majalisar Wakilai, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa fadar shugaban kasa ke yi musu jakkar baya wurin kin biyan jihohin da suka gudanar da ayyukan gwamnatin tarayya kudinsu kan lokaci.
Tambuwal ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bude hanyar da  ta tashi daga Jibiya zuwa Zurmi zuwa kauran Namoda ta wuce Gusau, wadda Gwamnatin Jihar Zamfara ta yi. Wannan hanya ta gwamnatin tarayya, an kaddamar da ita ne. wajen bikin cikarta shekara biyu bisa karagar mulkita.
“Mukan yi  bakin iyakacin kokarin mu don ganin  an biya gwamnoni kudin da suka kashe, amma abin sai ya ci tura, wannan yana biyo bayan turjiyar da suke samu daga fadar shugaban kasa,” inji shi.
Ya yi kira ga abokan aikinsa da su taimaka, su ga irin wannan matsaloli da ake samu, sun kau don a cewarsa hakan ne kawai zai sanya kwaliya ta biya kudin sabulu, wajen ganin  an rika biyansu, don samun nasarar ci gaba da irin wadannan ayyuka.
Wannan kalaman na Tambuwal sun biyo bayan rokon da Gwamnan  Jihar Zamfara ne ya yi, na cewa tun da ba wadannan ayyuka ne kawai a gaban jihar ba, yana rokonsa da ya gabatar da kokensa, don ganin an abiyasu.
Gwamnatin jihar ta bada wannan aiki ne kan kudi sama da biliyan biyu 2  da miliyan dari takwas, kuma cikin yardar  Ubangiji an samu nasara kammalata.