✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tare da Sheikh Yunus Is’hak Almashgool, Bauchi

53. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Anas dan Iyad ya ba mu labari daga Ubaidullahi daga Muhammad dan Yahya dan Habban daga…

53. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Anas dan Iyad ya ba mu labari daga Ubaidullahi daga Muhammad dan Yahya dan Habban daga Wasi’u dan Habban daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Na taba hawa saman dakin Hafsa sai na ga Annabi (SAW) yana biyan bukatarsa ta bayan gida, ya bai wa alkibla baya yana fuskantar Sham (Siriya).”

54. An karbo daga Ibrahim dan Munzir ya ce: “Anas dan Iyad ya ba mu labari daga Hisham daga babansa daga A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce: “Manzon Allah (SAW) ya kasance yana Sallar La’asar rana ba ta fita daga dakinta ba.”

55. An karbo daga Musa dan Isma’il ya ce: “Juwairiyyah ya ba mu labari daga Nafi’u daga Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Annabi (SAW) ya mike yana mai huduba sai ya yi nuni ta wajen dakin A’isha (yana nunin gabas) sai ya ce: “Fitina tana wannan bangare, har sau uku, ta wajen da kahon Shaidan ke bulla.” (Wannan ya nuna dakin A’isha ta gabas yake, yana nufin fitina daga gabas take ba daga dakin A’isha ba).

56. An karbo daga Abdullahi dan Yusuf ya ce: “Malik ya ba mu labari daga Abdullahi dan Abubakar daga Amrata ’yar Abdurrahman cewa: Lallai A’isha matar Annabi (SAW) ta ba ta labari cewa: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya kasance a wurinta sai ta ji muryar wani mutum yana neman izinin shiga dakin Hafsah sai na ce: “Ya Manzon Allah! Ga wani mutum yana neman izinin shiga dakinka. Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ina tsammani wane ne, baffan Hafsa ga shayarwa. Kuma ai shayarwar nono tana haramta abin da  haihuwa ke harramtawa.”

 

Babi na Biyar:

Abin da aka ambata game da taguwar (rigar) yaki (sulke) na Annabi (SAW) da sandarsa da takwabinsa da butarsa da zobensa. Da bayanin abin da halifofi suka yi aiki da shi a bayansa wanda aka ambata rabonsa. Kuma da bayanin gashinsa da dangarafansa (takalmansa) da kwaryarsa. Da bayanin abin da sahabbansa ke neman albarka da shi da wasunsa bayan rasuwarsa.

 

57. An karbo daga Muhammad dan Abdullahi mutumin Madina ya ce: “Babana ya ba mu labari daga Sumamah ya ce, Anas ya ba mu labari cewa: Lallai Abubakar (Allah Ya yarda da shi), ya ce: Lokacin da Abubakar aka halifantar da shi ya taba aika shi zuwa Bahrain ya rubuta masa wannan takarda (wasika) ya yi masa hatimi da hatimin Annabi (SAW). Kuma rubutun ya kasance layi uku ne na farko sunan: Muhammad, layi na biyu: Rasulu, layi na uku: Allah.”

 

58. An karbo daga Abdullahi dan Muhammad ya ce: “Muhammad dan Abdullahi Al’asadi ya ba mu labari ya ce, Isa dan Dahman ya ba mu labari ya ce: Anas ya fito gare mu da takalmar fata marasa gashi an yi musu ratsin fatu.” Bayan haka sai Sabit Albunani ya ba ni labari bayan haka daga Anas cewa: Haka takalmar Manzon Allah (SAW).”

 

59. An karbo daga Muhammad dan Bashar ya ce: “Abdulwahab ya ba mu labari ya ce, Ayyub ya ba mu labari ya ce, Humaid dan Hilal ya ba mu labari daga Abu Burdatu ya ce: “A’isha (Allah Ya yarda da ita) ta fito gare mu tana sanye da wata taguwar (rigar) ulu mai suna Mulabbadat . Kuma ta ce, “A cikin wannan taguwa ce aka karbi ran Manzon Allah (SAW), wato yana sanye da ita.” Abu Burdatu ya ce: “A’isha ta fito gare mu tana sanye da wata taguwar (rigar) sanyi mai kauri wadda aka yi daga gashin tumaki irin wadda ake sakawa a Yamen. Kuma wannan taguwa ita ce ake kira da sunan Mulabbadat.”

 

60. An karbo daga Abdan ya ce: “Daga Abu Hamza daga Asim daga Dan Sirin daga Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi), cewa: Lallai butar Annabi (SAW) an yi mata mariki da azurfa.” Asim ya ce: “Na ga butar kuma na sha daga butar.”