Search
Subscribe
Tashe-tashen gobara a kasuwar Abubakar Rimi Kano

Tashe-tashen gobara a kasuwar Abubakar Rimi Kano

Sama da Shekaru 35 Tsohuwar Gwamnatin Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi ta sake gini tare da tsarin Kasuwar Sabon Garin, sakamakon yawan tashin gobara, wadda akan alakanta ta da cunkushewar kasuwar tare da rashin tsaro.  An sake tsarin kasuwar ne da jan bulo (wanda wuta ba ta ci) ga manyan kofofi masu yawa, da masu gadi, har da offishin ’yan sanda, har lokacin shiga kasuwar da fita aka sama mata gami da hanyoyi masu yalwa, wanda motoci ka iya wucewa ba matsi, amma duk da haka wannan bai hana tashin gabora ba.
A Shekarar 1995 an sake tsarin kasuwar ta bangaren mallaka da gudanawa, inda aka mai da ita wani kamfani, wato Muhammadu Abubakar Rimi Market Ltd. Gwamnatin jiha da kananan hukumomin Birni da Dala da Fagged a Nassarawa da Gwale da Tarauni ke mallakar kasuwar, tare da tsarin gudanarwa mai kyau. Duk da haka wannan bai hana tashin gobara ba.
A Baya-bayan nan gwamnati ta sake kawata kasuwar, ta hanyar kara buda hanyoyin, tare da zuba musu interlock da jin dadin shiga da fita na motoci tare da al’umma.
A makonni da suka wuce ne aka ji mummunan labarin gobara, wadda ta shafe sama da awa 12 tana ci, zancen asarar dukiyoyi da aka yi. Kuma sanin haka sai Rabil izzati, fatan mu dai Allah ya mai da alheri.
Mafita:
A gaskiya asara ko ta mece ce ba ta da dadi ballanta na ta dukiya, wacce mutum ya sha wahalar Tarawa. Dubin yanayin kasuwar ya zama dole gwamnati ta yi karatun ta-nutsu don kare aukuwar irin wannan a nan gaba. Hanyoyin da za a bi kuwa sun hada da:
1. Hana yin kari a gaban rumfuna, wato ‘attachment.’
2. Hana kasa kaya a kan titunan kasuwar.
3. Tsugunnar da ’yan “attachment” a wani wurin daban a wajen kasuwar.
4. Kafa ofishin hukumar kashe gobara.
5. Samar da isassun kayan aiki ga hukumar kashe gobara.
Wannan ba zai samu ba sai an tabbatar da dokoki masu tsauri ga duk wanda ya yi biris da tsarin da aka shimfida.
Sannan ya zama dole gwamnati ta tabbatar da fara ginin kasuwar dangwauro, sannan kuma da kirkiro wasu kananan kasuwannin a gefen gari. Misali bangaren Dakata da dorayi/Panshekara da Gayawa/Pannisau/Jaba da Bachirawa/mil tara da sauran su.
A karshe ina mai yaba wa gwamnatin jiha da ta gaggauta kafa kwamiti, amma sai dai tsarin kwamitin ina ga bai yi ba. Don kuwa duk ’yan kasuwa ne, zai yi kyau a hada da hukumomi kamar haka:
1. Hukumar tsara birane ta KNUPDA
2. Ma’aikatar Kasuwanci da masana’antu, wato Ministry of Commerce
3. Hukumar tsaro
4. kananan hukumomin Fagged da Gwale da Dala da Birni da Nassarawa
Ina Fatan Allah ya kiyaye aukuwar irin wannan musifa ta gobara a gaba, Allah ya mayar musu da mafi Alheri.
Ana iya tuntubar Tijjani  Sarki ta sarkitijjaniabdullahi@yahoo.com

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin