Da Dumi Dumi

Tasirin ci gaban kimiyya da fasahar sadarwa ga zamantakewar dan Adam a duniya (1)

Mabudin kunnuwa

A cikin littafinsa mai suna: Our Posthuman Future: Consekuences of the Biotechnology Rebolution, wanda ya rubuta a shekarar 2002, Farfesa Francis Fukuyama ya shimfida bayanai kwarara kan hakikanin inda rayuwar dan Adam ke fuskanta da kuma inda ake sa ran za ta fuskanta nan gaba; a dunkule, yana hasashe ne, ta hanyar dalilai da hujjoji tabbatattu a lokacin da yake rubutu (2002), kan yadda rayuwa a wannan duniya za ta kasance, sanadiyyar tasirin ci gaban da ake samu a fannin Kimiyyar Sinadarai da Fasahar Kere-Kere, wato: Biotechnology. Ire-iren ci gaban da aka fara samu a lokacin da yake rubutun wannan littafi dai sun hada da magunguna ko kwayoyi masu sanya dan Adam farin ciki, da wadanda ke janye wa dan Adam bakin ciki da damuwa; ya ji ya koma wasai kamar ba abin da ke damunsa a rayuwarsa. Sauran sun hada da ci gaban da ake samu wajen iya canja sinadaran dabi’ar halittar dan Adam. Wannan tsari shi ake kira: “Genetic Modification,” ko “Genetic Engineering.” Wadanda suka saba karatun wannan shafi shekara 10 da suka gabata za su tuna makalolin da muka jero kan wannan maudu’i na sinadaran dabi’ar halitta, wato: “Genetics.”

Farfesa Fukuyama ya ce an fara tunanin canja sinadaran dabi’ar halittar dan Adam don gano nau’ukan kwayoyin halittar da ake haifar mutum da su masu haddasa masa cututtuka. Manufar ita ce a cire wadannan kwayoyin halitta, a canja su da wadanda ba su da matsala, don a haifi jariri salin-alin. Bayan wannan, an fara gano hanyoyin shigar da wasu dabi’o’i na musamman cikin kwayar halittar jariri gabanin a haife shi, don samar da ’ya’ya masu siffofi na musamman; kamar hazakar karatu da kaifin basira da saurin fahimta da kuma karancin mantuwa. Wannan ke nuna cewa nan gaba masu kudi za su rika zuwa wajen likitoci don a tsara musu ’ya’ya masu siffofi na musamman, wadanda ba za su kamu da cututtuka irin su cutar kanjamau ko sikila ko wasu munanan cututtuka ba.

A daya daga cikin shirye-shiryenta na mako a shekarar 2017, tashar rediyon BBC Inkuiry ta kawo bayanin wata fasaha mai suna CRISPR, wacce ita ce hanya mafi sauki da aka samar wajen iya nazarin sinadarai da kwayoyin halittar dan Adam da iya gano kwayoyin da suke da matsala da iya cire su da iya maye gurbinsu da wasu lafiyayyu, cikin sauki kuma ba tare da kashe kudade masu dimbin yawa ba. Samuwar wannan hanya a cewar masana, babban bala’i ne.  Domin kwararru marasa kishin jinsin dan Adam na iya amfani da fasahar wajen kasuwanci – ta hanyar samar da ’ya’ya masu siffofi na musamman. Wannan shi ake kira: “Designer Babies,” kamar yadda za ka iya zuwa kamfanin kera motoci ka musu bayanin irin motar da kake so; su kera maka ka biya.

A bangaren kwakwalwar dan Adam ma an samu ci gaba sosai. Makanta da kurumta sun kusa zama tarihi a rayuwar dan Adam ta yau da abin da zai biyo baya. Ana kan samar da sinadaran fasahar gani da wadanda suka shafi samar da kafar ji ga wadanda suke da matsalar gani da ji. Wadannan fasahohi dai ana shigar da su ne cikin jikin marar lafiya, su yi yawo a cikin jini don tantance bangarorin jijiyoyin kwakwalwar da ke da matsala, masu kashe ganinsa ko jinsa, sannan su maye gurbinsu da lafiyayyun jijiyoyin sadarwa da ake kira: “Neurons.”  Nan ba da dadewa ba za a samar da tsarin hada kwakwalwar dan Adam da na’urorin sadarwa, don tantance bugawar kwakwalwa da kokarin hararo tunani da manufa ko niyyar dan Adam.

ADVERTISEMENT

A cikin daya daga cikin shirye-shiryenta na watan Nuwamba mai suna: “Outlook”, tashar rediyo ta BBC World ta yi hira da wani likita da ya dasa wata na’ura a kwakwalwar wani bawan Allah dan kasar Faransa, wanda kafin wannan lokacin ya yi shekara kusan 10 ba ya iya motsa bangaren jikinsa na dama, sanadiyyar hadari da ya yi da mota.  Ana dasa masa wannan na’ura, nan take ta fara karanto bayanan da ke cikin kwakwalwarsa, wanda ta hakan ta gano jijiyoyin aika sakonnin da suka mace a kwakwalwarsa, ta dasa sababbi sannan ta fara taimaka masa iya motsa bangaren jikinsa da ya shanye.

Galibi a al’adar rayuwa mun san jinsin dan Adam guda biyu ne; namiji da mace.  Akwai wadanda Allah ke halittarsu da bangarorin duka jinsin. Amma a halin yanzu ci gaban kimiyyar halitta da sinadarai sun kai ci gaban da ake iya mayar da namiji ya koma mace-tare da dukkan bangarorin mace-kamar yadda ake iya mayar da mace ta koma namiji. Wannan tsari ya samo asali ne daga masu akidar kin wani jinsi da Allah Ya halicce su a kai. Wadannan su ake kira: “Non-Binary Gender Identities.”

Daga wannan mako in Allah Ya so, zuwa makonnin da ke tafe, za mu ci gaba da kawo bayanai filla-filla kan irin ci gaban da aka samu a baya da wanda ake samu yanzu a fannin kimiyya da fasahar sadarwar zamani, da abin da hakan zai iya haifarwa a siyasance ko addinance ko al’adance.

A mako mai zuwa za mu ci gaba.  A ci gaba da kasancewa tare da mu.

Share