Da Dumi Dumi

Taskar Filfilon Dausayin Kauna (FDK)

Ya ku masu bibiya tare da aiko sakonni a wannan fili, ina muku gaisuwa tare da jinjinar jimirin bibiya kuma ga wasu daga cikin sakonninku, kamar yadda aka saba:

 

Daga Abdulkadir Madaro Kurya (09038657194):

Assalamu alaikum FDK, barka da kokari. Ni kam ina goyon bayan Uwargida Farida.

 

ADVERTISEMENT

Daga Ibrahim Khaleel Jama’are:

Assalamu alaikum. A ra’ayina ina gidan Saratu, wato ina goyan bayan Alhaji Baba ya kara aure saboda ga dukkan alamu zai yi adalci a gidansa. Saboda haka ina goyon bayansa ya kara aure.

Daga Salisu Alkassim Tsakuwa (Abu Khalil):

Jinjina ga matata, uwar ’ya’yana, Mabaruka Garba Baba (Maman ’Yan Uku). Allah Ya jikan su Baba.

Daga Yasira Umar Legas:

Assalamu alaikum FDK, ina muku fatar  alheri da ma’abota bibiyar wannan shafi mai albarka na Dausayin Kauna. Wai shin me ya sa wadansu samari ke wasa da soyayyarsu?

Daga Maryam Danmakwayo Bauchi: Barka da warhaka da fatar FDK kana lafiya. Ina yi maka fatar alheri da fatar ka yi Sallar Juma’a lafiya.

Daga Gimbiya Asma’u Kano:

FDK, kishi kumallon mata ne amma duk da haka ina gidan Saratu, domin Allah bai yi namiji don mace guda ba.

Daga Isma’il Ali Kaduna:

FDK, Sardaunan masoyan wannan gida, ina so ka ba ni fili domin in yi tsokaci a kan masu bibiyar wannan gida mai albarka, ’yan uwana masoya a Dausayin Kauna. Ina shawartar junammu cewa ya kamata mu gina wata cibiya mai karfi, wadda kowa zai yi alfahari da ita a duniya da Lahira. Maza da mata da filfilo wato FDK, don Allah a yi nazari a kan sakona.

Daga Hafiz Abba Zariya (07034941358):

Ni fatar alheri zan muku FDK da irin dimbin gudunmawar da kuke bayarwa. Allah Ya bar zumunci, Ya kuma kara muku kwarin gwiwa.

Daga B. K. Kaduna:

FDK, ni dai Saratu Sak! Mata ku ba ni bayani, mece ce matsalarku da karin aure ne? Iyayenmu a gida da yaya ake hada su? Ku kuwa matan wannan zamani na karshen duniya, sai dai a raba muku gida ko ba halin haka. To, ku ji tsoron Allah mana!

Daga A. B. A Gangaren Pandogari:

Assalamu alaikum FDK da fatar kana lafiya, Allah Ya sa haka, amin. Ni dai ina gidan amarya Saratu. Ka huta lafiya FDK.

Daga Hameed Nura Fresh Boy (09067176209):

Godiya gare ka FDK da fatar kana lafiya, Allah Ya sa haka, amin. Ni dai ina bayan Farida, don haka kuri’ata na gare ta, tare da fatar alheri ga ’yan wannan fili.

Daga Nasiru Kainuwa Hadeja (08100229688):

Ina shawartar mata su rika lura da maza, duk namijin da zai taba jikinki ba son ki yake ba. Idan kuma ya nemi lalata da ke ko an sa ranar aurenku, ki rabu da shi, domin mutumin banza ne.

Daga Ahmad Yahaya G. (07062157794):

FDK, fatar alheri da dimbin godiya mai yawa. Ina yi wa abokiyata Khadija Abdullahi Abuja da sauran ma’abota bibiyar wannan shafi fatar alheri. Ni dai a gaskiya ina matukar goyon bayan Alhaji Baba da kuma amaryarsa Saratu.

Daga Amaryar Sarkin Kaya Musa:

FDK, ni sabuwa ce a wannan shafi kuma ma’abociyar bibiyar wannan shafi. Ina yi wa kowa fatan alheri. A ci gaba da ba mu shawarwari masu amfani, domin muna matukar karuwa da wannan shafi.

Daga Kueen Ayshart Abdulhameed Gombe (07034815180):

A gaskiya FDK, mu kam ba mu da abin da za mu ce maka sai dai godiya da kuma fatar alheri. Labarin Jidalin Kishiya kuma darasi ne a gare mu ga baki daya. Amma fa Aunty Farida ta yi hakuri, domin muna bayan Hajiya Saratu Amarya a gidan Alhaji Baba. Ina dago wa al’ummar garin Gombe hannu.

Daga Safiyanu S. Nuhu (08082262381):

FDK, gaskiya ina jin dadin Labarin Farida. Gaskiya yana sa ni nishadi sosai, sai dai fatar Allah Ya kara basira da nisan kwana mai amfani; Allah Ya daukaka Aminiya, amin.

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya