Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Tattaunawa da mawakin Hausa Musa Hassan

Hassan Musa Mawaki ne da ya kware wajen wakokin fina-finai, kamar kuma yadda yake wa ’yan siyasa da sauran al’umma. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana al’amura da suka shafi rayuwarsa da ta sana’arsa, kamar haka:

ADVERTISEMENT

 

Mawaki Hassan Musa tare da ‘yar fim Jamila NaguduWane ne Hassan Musa?
Ni mawaki ne ta bangaren siyasa da sauran bangarori amma abin da aka fi sani na da shi, shi ne harkar fina-finan Hausa, domin nakan fito a matsayin dan wasa da sauransu.

ADVERTISEMENT

Dalilinsa na shiga fim:
Da farko dai abin da ya ba ni sha’awa shiga harkar fim shi ne, tun lokacin da ina makarantar firamare wani malaminmu da ake kiransa Ibrahim Adamu Shigafarta da ke aiki da Gidan Rediyo Da Talabijin na Jihar Nasarawa, a lokacin shi ke jagorancin masu wasan kwaikwayo; ba na manta sunan makarantar Alfajarus Sadik Firamare. Daga nan sai mu kadan daga cikin matasan Lafiya muka kebe kanmu muka ce me zai hana mu dauki harkar fina-finai da sauransu a matsayin sana’a? Kodashike a lokacin ba a yin fim din Hausa sosai. Daga nan ne sai ina yin amfani da
basirar da na samu gun malamina da na bayyana maka, na kirkiro wata kungiyar matasan unguwarmu. Mukan hadu da dare mu je gun shi malamina, ranakun Asabar da Lahadi yana koyar da mu, har ma muka fara daukar hoto
muna tafiya jihohi daban-daban muna yi.
Ta bangaren waka kuma, a lokacin da na fara ba da umurni a wani fim dina mai suna ‘Iyali,’ bayan na fuskanci kalubale da dama a bangaren harkokin fina-finan, sai na zo na samu jari na saka. Tare da gudunmawar wasu mutane sai na fara ba da umurni ni da kaina, ba tare da na tuntubi shi malamina Ibrahim Adamu Shigafarta ba. Fim dina na ‘Iyali’ mun yi shi ne a nan Lafiya, wasu kuma mun je Kano. Mun yi aiki da su Sani Musa Danja da Mansura Isa da Saratu Gidado da Magaji Mijinyawa da dai sauransu a lokacin.
A tsakanin wannan lokacin ban soma rera wakoki ba amma ina rubutawa. Akwai wani mawaki a Kano mai suna Sani Hassan. Shi nake bai wa wakokina. Ina rubuta waka in kai masa ya rera. Wani lokaci ma idan na je wurinsa a Kano sai in kwana kamar biyu ina jiransa. Sai aka zo lokacin da aka fara zaben gwamna a jihar nan. Akwai wani maigidana da watakila ba zai so in ambaci sunansa ba. Ya tura ni na yi wata waka kan Injiniya Tanko Baba Abdullahi, shi ma ya nemi gwamna a lokacin. Da na rubuta sai na je Kano don Sani Hassan ya rera. Na ba da Karin wakar ga mai yi mana kida. Ya fara kida sai shi Sani da ya zo ya ji kidan ya ce bai yi masa ba. Kawai shi sai dai a canja kidan. Daga nan sai ya zama muhawara tsakaninsa da makadin ta sarke har shi Sani ya tafi ya bar mu. Ni kuma hankalina ya tashi don na kwana daya zai sake ja ni kwana biyu. Raina ya baci, shi ma makadin ya lura raina ya baci. Sai ya tambeya ni cewa kai Hassan ba kai ba ne kake rubuta wannan waka da kanka, don me kake damun kanka cewa wani sai ya yi maka? Me ya sa ba za ka rera wakar da kanka ba? Ya ce ina so ka gwada yau. Haka dai ya yi ta lallaba ni har a wannan lokacin na shiga studiyo na rera amshin wakar. Ina daura karin sai ya ce na fita. Da na fito sai ya fara gyara muryar, sai na ji na fara sha’awar muryar a lokacin. Da na sake shiga, dayake abu ne a rubuce, sannan kawai nan take na gama wakar. Ina fitowa mace ta shiga ta rera tata, sai na ga to ashe ina ma cutar kaina ne don muryata a wannan lokaci sai ta fi mini ta Sani Hassan. Da na dawo gida tun daga wannan lokaci ne na fara rera wakokina da kaina. Sau da yawa ma yanzu ba sai na rubuta ba nake rera wakokina.

Dalilin yin wakokin siyasa:
To a gaskiya abin da ya fara ba ni sha’awar yi wa Gwamna Almakura waka shi ne, kodashike a da ba na yi wa ’yan siyasa waka ko wani abu daban a saka a fim dina. Abin da ya ba ni sha’awar yi masa waka shi ne, akwai wani lokaci da na kai ziyara gidan wata kakata a Layin ’Yan Kaji a nan Lafiya. Ina zuwa hanyar unguwar sai na ga ta canja. Don da idan zan kai mata ziyara sai in ga mai kafa ma ba ya iya bin layin balle mai babur. To a lokaci daya sai na ga an kankare hanyar, an fara zuba mata duwatsu, ana gyara. Daga nan ne sai na ji ya fara ba ni sha’awa, sai na ji sonsa ya shiga min rai, kasancewa an yi
Gwamnatoci a baya amma ba su kula da wannan hanya ba sai a gwamnatinsa. To sai na ce ya kamata na yi masa wani abu.
Ina tunanin da me zan fara sai ya zo daidai da lokacin da aka fara maganar Boko Haram a arewacin kasar nan. A wannan lokaci ne na yi tunani, na ce to ga Boko Haram ya zo Arewancin Najeriya kuma Jihar Nasarawa na daya daga cikin jihohin Arewa. Sai na ce bari in yi wani abu game da zaman lafiya a jiharmu. Sai na hada wakar da kokarin da Gwamna Almakura ke yi wa jihar nan. Shi ya sa a cikin daya daga cikin wakokin da na yi masa za ka ji ina cewa: ‘Mai halin Sardauna gwamnatinsa ba barna. Sha gwagwarmaya tirmi sha daka Umaru maso talakawa.’ Yadda na fara shinfidata ke nan, ina kiran zaman lafiya a wakar, ina kuma tabo wasu nasarori da ya cimmawa. Ka ji abin da ya ba ni sha’awar yi masa waka ke nan. Kirkinsa ne ya sa nake masa waka kuma a yau idan zai daina ni ma zan daina yi masa waka, don ba na yi wa karya waka sai gaskiya.