✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

The Right Choice: Fim mafi girma a Kannywood da ya hada manyan jaruman Kudu da Arewa

A daidai lokacin da ake ta koke-koken tabarbaerwa harkokin kasuwancin fina-finan Hausa, shi kuwa Furodusa Abubakar Bashir Maishadda ba ya tsoron kashe kudi wajen shirya fim…

A daidai lokacin da ake ta koke-koken tabarbaerwa harkokin kasuwancin fina-finan Hausa, shi kuwa Furodusa Abubakar Bashir Maishadda ba ya tsoron kashe kudi wajen shirya fim a Masana’antar Kannywood.

A bara, Maishadda ya shirya fina-finai da suka hada da Mariya da Kanwar Dubarudu da Mudajala da Hafeez da Sareena da Hauwa Kulu da kuma Wutar Kara, inda duka ya samu nasara, kuma mutane suka yi ta yabawa, musamman ganin yadda fina-finan suka kyatar kuma suka nishadantar.

Ana cikin haka ne kuma kwatsam, sai Furodusan ya bayyana a watan Disamban bara cewa zai shirya fim da bai taba shirya kamarsa ba, kuma wanda ba a taba shirya kamarsa a Masana’antar Kannywood ba.

Hakan ya jefa masu kallo da sha’awar fina-finan Hausa cikin zullumi da jiran ganin fim din, wanda zai fi sauran da ya shirya.

Tun lokacin da kasuwancin fim ya fara tabarbarewa, wanda ya tursasa forudusoshi da dama  daina shirya fina-finai, wadansu kuma suka ajiye fina-finansu suka ki fitar da su, wadansu suka rufe ido suna fitar da fina-finan nasu.

Sai dai wadansu suna tunanin ko ana mayar da kudin da ake kashewa a fina-finan yanzu ganin cewa a sinima kawai ake haska fim din da sauransu, amma ganin ana kashe makudan kudi wajen shirya fina-finan, amma Maishadda ya ce zai yi wanda ba a taba yi ba, sai masu kallon suka fara tsimaya.

Abubakar Bashir Maishadda ya ce tare da Furodusa Kabiru Jammaje ne za su shirya fim din mafi girma a tarihin Kannywood.

Ya ce duk fina-finan da ya shirya da kuma nasarorin da ya samu kamar sharar fage ya yi.

Fim din mai suna The Right Choice, wato ‘Zabin da Ya Dace’ an shirya kashe masa zunzurutun kudi Naira miliyan 35, kuma ya kunshi manyan jaruman Kannywood da Nollywood wato na Kudu da Arewa.

Daga cikin jaruman fim din akwai Sani Mu’azu da Segun Arinze da Sola Sobowale da Nancy E.Isime da Enyinna Nwigwe da Ali Nuhu da Abba El-Mustapha da Asabe Madaki da sauransu kuma Ali Nuhu ne Daraktan Fim din.

Da Aminiya ta tuntubi Abubakar  Maishadda don ji ta bakinsa a kan  abin da ya sa fim din zai zama daban, lura da yadda ake ta maganar fim din, sai ya ce, “Fim din The Right Choice zai zama daban ne domin shi ne fim na farko da aka dauko jaruman Nollywood da dama, inda aka yi hadaka sosai da su, sannan lura da yanayi da lokacin da aka dauka ana yin fim din da yadda aka tsara shi da ma’aikatan da aka sa da abubuwan da fim din ke tattare da su da kuma yadda aka kawata shi, ya sa fim din ya bambanta da duk wani fim na Kannywdood, tun daga kashe kudi da kawata shi da sauransu.”

Game da abin da ya sa fim din zai fi girma a Kannywood, shin saboda yawan jaruman ne ko kudin da aka kashe ko saboda sakon da yake dauke da shi? Sai Maishadda wanda ake yi lakabi da Man Habu ya ce duk abubuwan da aka lissafo suna daga cikin abubuwan da suka sa fim din zai zama daban kuma ya zamo wanda ya fi girma.

“Tun kafa Kannywood, ba a taba kashe kudi a fim kamar kudin da aka kasafta kashewa wa fim din The Right Choice ba. Akwai tarin jarumai da aka dauko daga Nollywood da Kannywood, sannan bayan kudin, akwai batun sakon da fim yake dauke da shi. Duk wani mai kallon fim a  Afirka ta Yamma zai ji dadin fim din sosai. Labarin ne a kan wata ’yar jarida da ta shiga tashin hankali, kuma babbar jarumar ’yar Kudu ce,” inji shi.

Da aka sake tambayarsa ko zai mayar da Naira miliyan 35 da ya kasafta kashewa a fim din, sai ya ce ai komai Allah kadai Ke tsarawa, “Sosai ma ina sa ran zan dawo da kudin har ma in samu ninkin-ba-ninki na riba. Ka san komai Allah ne Yake tsarawa. Kai dai iya naka shi ne ka yi tsari mai kyau, kuma ka yi bincike mai kyau. Amma ai Allah Ya riga Ya kaddara komai. Kuma cikin ikon Allah, muna sa ran ba ma dawo da kudin da muka kashe ba, da yardar Allah za mu samun ninkin riba,” inji Maishadda.

Fim din wanda yanzu haka an kammala daukar zagaye na farko, saura zagaye na biyu ana sa ran za a kaddamar da haska shi a watan Disamba mai zuwa ne a sinima wato nan da wata 10.

Daya daga cikin jaruman da suka taka rawa a fim din wadda kuma ita ce ta ja fim din, wadda ta zo daga Nollywood, Nancy E. Isime ta ce ta ji dadin yadda aka tsara da kuma yadda aka dauki fim din. Kuma ta dajin fitowarta a matsayin Hajiya.

Nancy, wadda ta taba lashe gasar Sarauniyar Kyau ta Balentine International Beauty Peagent a shekarar 2009, ta ce, “Na kammala nawa aikin wajen daukar fim din The Right Choice. Na yi matukar jin dadin yadda na kasance Hajiya na mako biyu. Jinjina ga Furodusan Fim din, Abubakar Bashir Maishadda da Darakta Ali Nuhu, da sauran jarumai da ma’aikatan fim din. Ina godiya mutanen Abuja da Legas ga ni nan zuwa,” inji ta.

 

Ta lashe kyaututtuka da dama kan kasancewarta jaruma, ciki har da Jaruma Mai tasowa ta City People Mobie Awards da ta lashe bara da sauransu.

Sola Sobowale, ita ma fitacciyar jaruma ce, furodusa kuma darakta a Masana’antar Nollywood. Daga cikin fina-finanta akwai Ohun Oko Somida da ta shirya kuma ta bada umarni a shekarar 2010.

Enyinna Nwigwe, fitaccen jarumi kuma furodusa da ke jan zarensa a Nollywood. A shekarar 2017, News of Africa ta bayyana shi a matsayin na daya a cikin kwawawan jarumai 12 a Masana’antar Nollywood.

Segun Arinze, wanda sananne ne a Masana’ntar Nollywood ya dade yana jan zarensa musamman a fina-finan mugunta da sauransu. Ana yi masa lakabi da Balck Arrow tun a zamanin da.

A bangaren Kannywood kuma, akwai manyan jarumai irin su Ali Nuhu da Sani Mu’azu wanda shi ma ya dade yana fitowa a fina-finan Hausa da Ingilshi da Abba El-Mustapha da Rabi’u Rikadawa da Asabe Madaki da sauransu.

Shi dai fim din The Right Choice, labari ne a kan wata matashiyar ’yar jarida Nanjala (Nancy E. Isime) da aka haifa kuma ta taso a Arewa.

Tana shiga matsala a harkar aikinta na jarida, amma ta tsaya kai- da-fata a kan bin doka da ka’idojin aikin da take yi ba tare da tsoro ba.

Abubakar Bashir Maishadda da Kabiru Jammaje ne suka dauki nauyin fim din. Zahradden Ibrahim Kalla ya bada labarin, Shariff Aminu Ahlan ya tsara shi, Aminu S. Bono ne Mataimakin Mai Bada Umarni, sannan Ali Nuhu ya bada umarni.