✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tom Starke: Tsohon golan Bayern Munich da ya lashe kofuna 14 a wasanni 12 da ya buga

A yau ne tsohon golan kungiyar Bayern Munich da kasar Jamus, Tom Starke ke bikin zagayowar ranar haihuwarsa. Tom ya cika shekara 39 ke nan,…

A yau ne tsohon golan kungiyar Bayern Munich da kasar Jamus, Tom Starke ke bikin zagayowar ranar haihuwarsa.

Tom ya cika shekara 39 ke nan, kasancewar an haife shi a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 1981.

Ya kama wa kungiyoyi guda shida gola a shekara 18 da ya yi yana tsaron gida.

Wani abin mamak shi ne yadda tsohon golan ya lashe kofuna guda 14 a shekara shida da ya yi a kungiyar Bayern Munich, duk da cewa wasa 12 kawai ya buga wa kungiyar, kamar yadda Wikipedia ya tabbatar.

Yanzu haka Tom shi ne mai horar da masu tsaron gidan kungiyar Bayern Munich.