✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Torino ta sayi dan kwallon Najeriya Ola Aina a kan Naira Biliyan 4

Kulob din Torino da ke wasa a gasar rukuni-rukuni ta  Italiya da aka fi sani da Serie A ta saye dan kwallon Najeriya Super Eagles…

Kulob din Torino da ke wasa a gasar rukuni-rukuni ta  Italiya da aka fi sani da Serie A ta saye dan kwallon Najeriya Super Eagles Ola Aina daga kulob din Chelsea da ke Ingila a kan Fam Miliyan 10 kimanin Naira Biliyan 4 da Miliyan 710.

Ola Aina, wanda yake daga daga cikin ’yan kwallon da ke yi wa Super Eagles kwallo, a bara ne kulob din Chelsea na Ingila ya tura shi kulob din Torino na Italiya a matsayin aro.  Ganin yadda tauraruwarsa ta haskaka a kakar wasan da ta wuce inda ya buga wa Torino wasanni 32 kuma ya taimaka wajen zura kwallaye uku (assists) a raga ya sa kulob din yanke shawarar ya saye shi a matsayin na dindindin, ba aro ba.

Ola Aina, dan shekara 22 yana buga kwallo ne a  a bangaren baya (Full-back) kuma yana daga cikin ’yan kwallon da ake sa ran za su wakilci Najeriya a gasar cin kofin Afirka da za a fara a ranar 21 ga wannan wata a Masar.