✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsarin Ma’adanar Bayanai a Kimiyyance (6)

Sai kashi na biyar, wanda ake kira: DBD-RW, wato: “Rewritable” ke nan.  Abin da wannan kalma ke nufi shi ne, kana iya goge bayanan da…

Sai kashi na biyar, wanda ake kira: DBD-RW, wato: “Rewritable” ke nan.  Abin da wannan kalma ke nufi shi ne, kana iya goge bayanan da ka zuba a ciki, sannan ka sake zubawa ko taskance wasu. Shi ma wannan nau’in DBD ana sayensa ne holoko; babu komai a ciki. Idan ka saya, sai ka zuba bayanan da kake bukata. In ka ga dama kuma ka goge su kai-tsaye. Sai kashi shida da ake kira: DBD-RAM, wato: “Random Access Memory.”  Wannan nau’i na DBD kuma ana amfani da shi ne a kwamfuta kadai. Faifai ne na DBD wanda ke matsayin ma’adanar wucin-gadi, wato: “RAM” ke nan. Idan aka dora wa kwamfuta, ba a cirewa sai an kashe, misali. Shi ma ba a iya goge bayanan da ke cikinsa.

Bayan wadannan, akwai wadanda suka kebanci kwamfuta ne zalla. Wadannan su ne masu tagwayen faifai, wadanda mizaninsu mafi karanci shi ne tiriliyan takwas da digo biyar (8.5GB). Daga ciki akwai nau’in DBD+R, wanda shi kuma yakan zo ne da bayanai a cikinsa, amma kuma a kwamfuta kadai ake iya sarrafa su. Kuma ba a iya goge abin da ke ciki, saboda a kulle suke. Kusan iri daya da nau’in DBD-R ke nan, bambancinsu kawai shi ne, shi DBD-R kan zo holoko ne, babu komai a ciki. Sai kuma nau’in DBD+RW, wanda shi kuma ke zuwa da bayanai a ciki amma a kwamfuta ake iya sarrafa su. Wadannan nau’uka dai masu dauke da tagwayen faifai ne, wato: “Dual Layer DBD.”  Suna amfani ne da wani tsari mai suna: “Opposite Track Path,” wajen sarrafa bayanan sauti ko bidiyo da suke dauke da shi. Idan faifan farko ya kare, nan take sai wannan tsari na OTP ya yi farat ya tsallaka zuwa titin da ke dauke da faifan bayanai na biyu, don ci gaba.

Girma da yanayi

Ta bangaren zahirin siffa, faifan DBD ya kasu kashi biyu, nan ma. Kashin farko su ake kira: “MiniDBD,” masu karamin ruwa ke nan. Galibi ba su shahara a kasashenmu ba, sabanin na biyun. Nau’in MiniDBD sun kasu kashi 4 ne. Akwai MiniDBD-1, mai girman mizani 1.4GB.  Sai MiniDBD-2, mai girman mizani 2.65GB.  Sai MiniDBD-3, mai girman mizani 2.92GB. Sai kuma na karshe, wato MiniDBD-4, wanda ke dauke da mizani 5.31GB.  Daga nau’in MiniDBD-1 har zuwa MiniDBD-4, duk girman jikinsu daya; mizani ne kawai ya bambanta su. Fadinsu duk bai wuce santimita 8 (8cm) ba.

Nau’i na biyu kuma su ake kira: “Standard DBD”; su kuma sun kai guda biyar, ta la’akari da mizaninsu. Akwai DBD5, mai mizanin 4.7GB.  Wannan shi ne wanda ya shahara a kasashenmu. Sai kuma DBD9, mai girman mizani 8.54GB. Wannan galibi akan same su ne dauke da manhajojin kwamfuta. Sai DBD10, wanda ke dauke da mizani 9.40GB.  Sai DBD14, mai dauke da mizani 13.24GB. Sai na karshe, wato DBD18 wanda ke dauke da girman mizani 17.08GB. Su ma, kamar kashi na farko, daga DBD5 zuwa DBD18, duk girmansu daya. Mizani ne kadai ya bambanta su. Fadinsu ya kai santi-mita 12, (12cm).

Tsarin Sarrafa Bayanai

Fasahar faifan DBD ta fi ta CD inganci da kuma gaggawar sadar da bayanai wajen taskancewa, ko wajen nunawa da bayyanawa. A yayin da fasahar CD ke cillo haskenta don taskance bayanai a tazarar nanometer 780 (780nm), fasahar DBD na cillo haske ne a tazarar nanometer 650 (650nm). Dukansu suna amfani ne da hasken lantarki nau’in leza, mai launi ja. Sinadaran da ke cikin hasken sun dara karfin sinadaran hasken infra-red.

SANARWA

Ina fadakar da masu karatu sauyin adireshin Imel don aiko sakonni gare ni. A baya shafin na amfani ne da adireshin: [email protected] <mailto:[email protected]>. A halin yanzu, sanadiyyar Gidan Yanar Sadarwar da na bude wanda ke dauke da dukan kasidun da suke bayyana a wannan shafi, na sauya sabon adireshin. Masu karatu na iya tuntubata ta sabon adireshin wannan shafi kamar haka: [email protected] <mailto:[email protected]>. Ina godiya matuka da sakonninku.  Allah Ya sa mu dace, amin.

 

karancinsa domin wadanda suke saye a wajensu a dazuzzukan su ma sun mayar da hankalinsu wajen aikin wake ko gero a lokacin suna wahala turmin ba ya samuwa.